Kwamandan ’yan sandan Kafanchan ya bukaci a guji tada rikici a lokacin zabe

Kwanmandan ’Yan sandan Shiyyar Kafanchan da ke Jihar Kaduna Alhaji Abdullahi Ibrahim ya bukaci matasa da ’yan siyasa su guji tayar da rikici a lokacin zaben da za a gudanar gobe a kasar nan da kuma na ranar 11 ga Afrilu mai zuwa. Alhaji Abdullahi Ibrahim ya yi wannan kira ne a lokacin da yake […]

Kwamandan ’yan sandan Kafanchan ya bukaci a guji tada rikici a lokacin zabe
Kwamandan ’yan sandan Kafanchan ya bukaci a guji tada rikici a lokacin zabe

Kwanmandan ’Yan sandan Shiyyar Kafanchan da ke Jihar Kaduna Alhaji Abdullahi Ibrahim ya bukaci matasa da ’yan siyasa su guji tayar da rikici a lokacin zaben da za a gudanar gobe a kasar nan da kuma na ranar 11 ga Afrilu mai zuwa.

Alhaji Abdullahi Ibrahim ya yi wannan kira ne a lokacin da yake jawabi ga shugabannin siyasa da na addini da kungiyoyin matasa da ’yan sanda a garin Saminaka, a ci gaba da ziyarar da yake yi a shiyyarsa kan zaben da za a gudanar.
Kwamandan ya ce Allah Ya riga Ya zabi wanda zai yi nasara a zaben da za a gudanar don haka yana kira ga sarakuna da shugabannin addini da na al’umma da ’yan siyasa da shugabannin kungiyoyi su jawo hankalin matasa, su guji tayar da rikici a lokacin zaben da bayansa.
Ya ce zaman lafiya da kwanciyar hankali ya fi komai, don haka yadda aka yi yakin zabe lafiya ya kamata a yi zaben lafiya.
Ya ce aikin samar da tsaro hakki ne da ya rataya a wuyan kowa a kasar nan, don haka jama’a su rika bai wa jami’an tsaro goyon baya da hadin kai a aikin samar da tsaro.
A jawabin Babban Jami’in ’Yan sandan karamar hukuma SP Ibrahim Usman ya gode wa al’ummar yankin kan goyon baya da hadin kan da suke bai wa jami’ansa.
Ya ce “Allah Ya taimake mu a yankin Saminaka duk da ya yi iyaka da jihohin Filato da Bauchi da Kano ana zaune lafiya, sakamakon goyon baya da hadin kan da muke samu daga jama’a.”
A jawaban shugaban kungiyar Jama’atu Nasril Islam na karamar hukumar kuma Limamin Saminaka Imam Shu’aibu Liman da shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen karamar hukumar Rabaran Tutu, sun cewa babu shakka hakki ne a kan shugabannin addini su tabbatar kasar nan ta zauna lafiya. Sun ce za su yi kokari wajen gudanar da addu’o’i da jawo hankalin jama’a kan muhimmancin zaman lafiya.