Kwamandoji da ’yan Boko Haram sun shiga hannu
Hukumar Tsaron kasa (SSS) ta bayyana kama kwamandojin kungiyar Boko Haram da wasu ’ya’yan kungiyar a jihohin Legas da Enugu da Kano da Filato da Gombe a tsakanin 20 ga Yuli zuwa Agustan bana. Wata sanrawa da ta fito daga kakakin hukumar Mista Tony Opuiyo ce ta bayyana haka inda ta ce cikin wadanda aka kama […]
Hukumar Tsaron kasa (SSS) ta bayyana kama kwamandojin kungiyar Boko Haram da wasu ’ya’yan kungiyar a jihohin Legas da Enugu da Kano da Filato da Gombe a tsakanin 20 ga Yuli zuwa Agustan bana.
Wata sanrawa da ta fito daga kakakin hukumar Mista Tony Opuiyo ce ta bayyana haka inda ta ce cikin wadanda aka kama har da wanda ya tsara hare-haren bam a Potiskum da Kano da Zariya da Jos.
Wadanda aka kama sun hada da: Usman Shu’aibu (da ake wa lakabi da Money): Shi ne ya tsara hare-haren Potiskum da Kano da Zariya da Jos da aka ce wani Amir dinsa mai suna Isa Ali ya biya Naira dubu 500, don aiwatar da hin Jos. Ya ce Isa Ali yana da alaka da Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, inda ya karbo kudin don aiwatar da Markaz dinsu ta dauki nauyin gudanarwa. Kuma ya ce ya taka rawa a hare-haren da kungiyar ta kai ciki har da na Babban Ofishin ’Yan sandan Gwoza a shekarar 2014.
Ya yi ikirarin cewa shi ne jagoran tawagar ’ya’yan kungiyar tara da aka turo daga dajin Sambisa su kai hare-haren, inda hudu daga cikinsu aka yi amfani da su wajen kai harin kunar bakin wake.
Sai kuma Ahmed Mohammed (da ake wa lakabi da Abubakar), wanda kwararre ne wajen hada bama-bamai, wanda ya hada bama-baman da aka kai hare-haren da aka ambata. Kuma ya tabbatar shi yake daura bama-bamai a jikin wadanda suka kai harin kunar bakin wake na Jos. Akwai kuma Adamu Abdullahi (da ake wa lakabi da Bappa). Wanda ya furta cewa Usman Shu’aibu ne ya ja ra’ayinsa ya yi aiki da Ahmed Mohammed (Abubakar) wajen tsara bama-baman da aka yi amfani da su wajen kai hare-haren.
Ibrahim Isa, wanda ya yi ikirarin yana daya daga cikin wadanda suka nazarci yadda za a kai harin na Jos kafin a kai shi.
Sai kuma Muttaka Yusuf (da ake wa lkabi da Mohammed Sani ko Muttaka), wanda ya ce wani mai suna Aliyu, wanda ake da yakinin Aliyu Gombe, a dajin Sambisa ne da ya bayar da umarnin kai hare-haren da kungiyar ta kai. Ya furta cewa ya taimaka wa Usman Shu’aibu wajen aiwatar da hare-haren.
Mambobin kungiyar da aka kama a Jihar Legas sun hada da Bakura Modu – wanda aka kama ranar 20 ga Yuli a Karar Isheri Berger a karamar Hukumar Ikeja, sai Mustapha Alli Jamneri da aka kama a ranar 24 ga Yuli a rukunin gidaje na Gowon Estate, Egbeda, karamar Hukumar Alimosho, sai Abuyi Sheriff – da aka kama ranar 7 ga Agusta, 2015, a Ebute-Metta, a karamar Hukumar Legas Mainland da Babagana Ali da Babagana Koloye – da aka kama su rana daya (7 ga Agusta), a Eric Moore, titin Bode Thomas, karamar Hukumar Surulere LGA da Abba Modu Sagma da aka kama a ranar 0 ga Agusta a Ijora Badiya, karamar Hukumar Apapa, sai Girema Abubakar da Tijjani Bagudu da aka kama su a ranar 10 ga Agusta, a Amukoko, Ijora Badiya, karamar Hukumar Apapa.
Akwai Baba Alhaji da Abass Ibrahim da aka kama su a ranar 10 ga Agusta, a Kasuwar Alaba International Market, Alaba, karamar Hukumar Ojo, duk a Jihar Legas.
An kama Ibrahim Audu a ranar 19 ga Agusta, a New Artisan Market da ke Enugu a Jihar Enugu, sai Ibrahim Haruna mai shekara 30 daga kauyen Kanawa a karamar Hukumar Sumaila a Jihar Kano wanda aka kama a ranar 21 ga Agusta a Kwami da ke karamar Hukumar Kwami ta Jihar Gombe.
Sai kuma Malam Ali Mohammodu mai shekara 33 da aka kama a ranar 22 ga Agusta a titin Ibrahim Taiwo Road, a karamar Hukumar Fagge a Jihar Kano. Akwai kuma Adam Wakil Abdul Jibbar da aka kama a ranar 23 ga Agusta, a yankin Obanikoro da ke karamar Hukumar Mushin a Jihar Legas da Mohammed Usman wanda aka kama a ranar 25 ga Agusta a rukunin gidaje na Atuashe Estate, Gbagada, karamar Hukumar Kosofe a Jihar Legas.