Kwamandojin Boko Haram da Mayaka 49 Sun Mika Wuya A Borno
Boko Haram da ISWAP na yakar juna saboda mata da kudi da yankunan da suke da iko Arewa maso Gabas
Manyan kwamandojin kungiyar Boko Haram da suka hada da Ba’a Usman (Munzir) da Alhaji Ari (Nakib) da wasu mayakan kungiyar 49 sun mika wuya ga sojojin Najeriya a Jihar Borno.
Wata majiyar soji ta shaidar mana cewa ’yan ta’addar sun mika wuya ga sojojin Operation Hadin Kai ne a Damboa a ranar Lahadi.
- Kaso 60 na ’yan Arewa ba su da asusun ajiya na banki – Uba Sani
- Qatar 2022: Mun sayar da tikitin kallon kwallo guda 3m –FIFA
Rahoton ya nuna maharan sun fito ne daga maboyarsu da ke Dajin Sambisa, suka kai hare-hare kan sojoji da kauyukan da ke kewaye da dajin.
Akalla ’yan tada kayar bayan 90,000 da iyalansu ne mika wuya ga rundunar sojin Najeriya ya zuwa yanzu, kamar yadda kwamandan rundunar OPHK Manjo-Janar Christopher Musa ya bayyana.
Aminiya ta samu labarin cewa ci gaba da kai hare-haren da sojoji ke kaiwa masu tada kayar baya ya tilasta musu da mika wuya.
Hakan ya faru ne yayin da kungiyoyin ’yan ta’adda na Boko Haram da ISWAP ke ci gaba da fafatawa da juna kan kudi da mata da kuma yankunan da suke da iko a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.