‘Kwamandojin mayakan IS sun shiga Libya’
Wani jami’in Leken asirin Libya ya fadawa BBC cewa a ‘yan watannin nan kwamandojin mayakan kungiyar IS sun shiga cikin kasar daga kasashen Siriya da IrakiIsma’il Shukri– wanda shi ne shugaban hukumar leken asiri ta garin Misrata, ya ce wasu mayakan kungiyar ta IS sun shiga kasar.Ya ce shigowar ta su, ta biyo bayan matsin […]
Wani jami’in Leken asirin Libya ya fadawa BBC cewa a ‘yan watannin nan kwamandojin mayakan kungiyar IS sun shiga cikin kasar daga kasashen Siriya da Iraki
Isma’il Shukri– wanda shi ne shugaban hukumar leken asiri ta garin Misrata, ya ce wasu mayakan kungiyar ta IS sun shiga kasar.
Ya ce shigowar ta su, ta biyo bayan matsin lambar da kungiyar ke fuskanta a yankin Gabas-ta-Tsakiya, inda kasashen duniya ke yi musu luguden wuta ta sama da kuma ta kasa.
Mista Shukri ya ce mayakan IS na daukar Libya a matsayin inda za su tsira da rayukansu
Libya dai ta shiga fada cikin rikici ne tun lokacin da aka hanbarar da Kanar Gaddafi a shekarar 2011.