Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa

TarihinaDa farko dai sunana Fadimatu Abdul-Aziz Yari, ni mutuniyar Jihar Zamfara ce. An haife ni a garin Talatan Mafara a shekarar 1970, sunan mahaifina Alhaji Salisu  Abdullahi. Ni ce diyar farko a wurin mahaifiyata kuma ina da kanne tara. kuruciyataTarbiyyar da iyayena suka yi mini shi ne na kasance yariya mai biyayya; na rike kalmar […]

Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa

n Hajiya Fdimatu Abdul Aziz Yari Tarihina
Da farko dai sunana Fadimatu Abdul-Aziz Yari, ni mutuniyar Jihar Zamfara ce. An haife ni a garin Talatan Mafara a shekarar 1970, sunan mahaifina Alhaji Salisu  Abdullahi. Ni ce diyar farko a wurin mahaifiyata kuma ina da kanne tara.

kuruciyata
Tarbiyyar da iyayena suka yi mini shi ne na kasance yariya mai biyayya; na rike kalmar daraja na gaba ni da muhimmanci har yanzu. Lokacin da nake tasowa, na taba zama da kakata, sunanta Amina. Ni ce diyar da tafi kauna saboda irin kulawar da nake samu daga gareta. Ta koyar da ni ilimin addini, soboda haka aka sanya ni a makarantar Islamiyya da wuri. Lokacin nan, iyayena sun yi amannar cewa ilimin boko ga diya mace bata lokaci ne, hakan ya sa suke boye mu a cikin gida duk lokacin da jami’an gwamnati suka bukaci a sanya mu a makaranta, wannan ya sa karatun Islamiyya na yi kawai. Amma bayan kakata ta rasu,na koma wajen iyayena a garin Jos, lokacin na girma kwarai hakan ya sa sai kawai na ci gaba da karatun Islamiyya.
Har yanzu ba na manta lokacin da nake karama, lokacin da muke zuwa kogi da sa’o’ina.  Wannan wani abu ne na kuruciyata da ba zan manta ba, saboda a yanzu da wuya kake ganin yara suna wasa, kuma ma idan ka gani da wuya ka ga an bar yaro ya tafi kogi saboda hadarin da ke tattare da hakan.

Burina lokacin da nake karama
Lokacin da nake yarinya, ina da burin zama ma’aikaciyar lafiya ce, da a ce na samu damar halartar makarantar boko, a gaskiya da zan zama likita ce saboda a kasar nan musamman nan yankin Arewaci, idan ba a ’yan kwanakin nan ba, ba a da wadatattun likitoci mata, galibinsu maza ne. Saboda haka da a ce zan iya dawo da jiya yau, to da zan koma na karanci aikin likita ne.

Kasancewata uwa
Kasancewata a matsayin uwa abu ne mai dadi, wani abu da kowace mace take matukar kauna kuma ina godiya da Allah Ya azurtani da ’ya’ya nagari. Haihuwata ta farko ta zo mini da sauki. Ban fuskanci wata babbar matsala ba lokacin haihuwa, gaskiya ina gode wa Ubangiji, saboda lokacin da nake dan fuskantar matsala shi ne watanni na farko na samun juna-biyu wadda kuma galibin mata suke fuskanta, amma da zarar junan biyun ya kai watanni hudu kuma sai jikin ya daidaita. Ina da ’ya’ya takwas, kuma daya ma har ya yi aure, kallon tasowarsu kawai wani abu da ke sa ni farin ciki.

Yadda nake taimakon mata da kananan yara a Jihar Zamfara
Na mayar da taimako  jiki, wato ina kai ziyara gidajen marayu don in taimaka musu ta hanyoyin da zan iya. Kwana-kwanan na shirya wani taron iyaye mata a tsakankanin kananan hukumomi 14 da ke jihar nan. Kuma ina shirin bullo da wasu hanyoyi don taimakon mata a jihar saboda a kowace al’ummar da ka samu kanka, mata suke taka muhimmiyar rawa, don haka ba za mu iya watsi da muhimmancinsu a al’umma ba.

Yadda na hadu da mai gidana
An hadu da mai gidana ne shekaru masu yawa da suka wuce. Gidansu ba shi da nisa daga namu saboda haka mu ba bakin juna ba ne. Amma a ranar da muka fara haduwa yana kan hanyarsa ne ta zuwa makarantar Islamiyya lokacin ni kuma ina dawowa daga kogi, sai ya yi mini magana kuma sai komi ya tafi daidai. Saboda gidanmu da idansu sun fahimci juna, bayan wani dan lokaci sai aka daura mana aure.

Halayen mai gidana da suka fi burgeni
Mai gidana mutum ne da yake da kirki matuka, kuma mai hakuri ne da kaunar addini. Mutum ne mai kulawa da duk wanda yake kusa da shi.

Kyautar da ya taba yi mini da ba zan manta da ita ba
Kyautar da ya taba yi mini da ba zan manta da ita ba ita ce soyayyarsa da kuma goyon bayan da yake ba ni kusan kan komi. Yana ba ni goyon baya kusan kan komai da na sanya a gaba kuma hakan ya sa nake godiya a gare shi. Wata karin kyautar da na samu daga gare shi ita ce kyautar ’ya’ya. Ina ganin kyawawan dabi’unsa a wurin ’ya’yana kuma ina godiya ga Allah da Ya ba ni ’ya’ya nagari.

Abin da nake yi idan ba na aiki
Nakan zauna ne tare da kowa da kowa a daki don tattauna yadda al’amura suka kasance. A wasu lokuta kuma mukan zauna ne mu kalli fina-finan don asamu nishadi akwai lokacin da har da shi kansa mai gidan.

Wuraren da ma fi so na ziyarta
Na fi so na ziyarci birnin Dubai na kasar Hadaddiyyar Daular Larabawa (UAE) saboda yana da manyan kantuna da dama da ake yin sayayya kuma ina kaunar yanayinsu saboda yana kama da na mu. Har ila yau, kasar Amurka wuri ne mai kyau kuma ina son mutanen can. Sai dai babu wurin da ya kai gida dadi. Gaskiya ina son nan gida Jihar Zamfara.

Yadda nake kwalliya
Ina son na yi kwalliya matsakaiciya wadda ba ta saba wa addinin Musulunci ba. Ina sha’awar sanya atamfa sosai. Hakazalika, tufafinmu na ’yan Afirka saboda suna kara wa mace kyau.

Irin kayan kwalliyar da nake amfani da su
Ina son sanya warwaro da zobe da abin wuya da kuma jaka.

kalubalen da nake fuskanta a matsayina na matar gwamna
A kowane irin hali mutum ya samu kansa ba ka raba shi da kalubale. Za ka so ka taimaki duk wanda ya tunkaroka don neman tallafi, amma matsalar ita ce wani idan ka bincika sai ka ga labarin da ya shaida maka ba gaskiya ba ne. Kodayake, abin da nake yi shi ne nakan bi sahun abin da aka fada mini don tabbatar da hakan gabanin na taimaka. Saboda babban kalubalen da nake fuskanta shi ne wajen taimakon jama’a wato ta bangaren tantace sahihan masu bukatar tallafi.

Mutanen da nake koyi da su
Akwai Baba Yari wato surikina. Wannan dattijon mutumin kirki ne matuka, yana hulda da kowa ba tare da la’akari da matsayin mutum ba. Yana matsayin mahaifi ne a wurina saboda yadda ya dauke ni tamkar diyarsa ta cikinsa. Babu abin da zan ce sai dai Allah Ya jikansa da rahma. Baba yana da rikon gaskiya, hakan ya sa nake fatan karasa rayuwata ta hanyar koyi da halayensa.

Abincin da na fi so
Kwadon zogale

Shawarwarina ga mata
Ya kamata mu   san muhimmancin hakuri a rayuwa saboda idan ba ka da hakuri ba za ka taba cimma burinka ba. Saboda haka nake kira ga mata ’yan uwana da su kasance masu hakuri da juna musamman a gidajensu.

Abin da nake so a rika tuna ni da shi
Ina so a rika tuna ni da wadda take tallafa wa masu bukatar taimako.

Darasin da na koya daga kakata wanda ba zan manta da shi ba
Kamar yadda na bayyana da farko, kakata ta ba ni tarbiyya na kasance mai biyayya ga nagaba da ni da kuma taimaka wa mabukata.

Darasin da na koya daga rayuwa
Rayuwa ta koya mini daraja kowa da zuciya guda.