Kwamashinan Shari’a ya damu kan yawaitar fyade a Jigawa
Kwamashinan Shari’a na Jihar Jigawa Barista Yakubu A. H. Ruba ya nuna damuwa game da yadda ake samun yawaitar laifuffukan fyade a jihar musamman ga kananan yara. Kwamishina Yakubu Ruba ya fadi haka ne a wani taron manema labarai da ya kira ranar Larabar da ta gabata a ofishinsa, inda ya kuma nuna damuwa kan […]
Kwamashinan Shari’a na Jihar Jigawa Barista Yakubu A. H. Ruba ya nuna damuwa game da yadda ake samun yawaitar laifuffukan fyade a jihar musamman ga kananan yara. Kwamishina Yakubu Ruba ya fadi haka ne a wani taron manema labarai da ya kira ranar Larabar da ta gabata a ofishinsa, inda ya kuma nuna damuwa kan yadda wasu kungiyoyin kare ’yancin dan Adam suke wa tsarin shari’a hawan kawara a jihar musamman a kan hukuncin da kotu ta yanke wa mutumin da ya yi ikirarin ya yi fyade ga wata karamar yarinya a karamar Hukumar Birniwa da kotun ta ce a jefe shi har sai ya mutu. Ya ce kotun ta yanke masa hukuncin ne saboda ikirarin aikata laifin da bakinsa amma saboda shigowar kungiyar kare ’yancin dan Adam aka canja hukuncin zuwa dauri a gidan maza. Ya kara da cewa ma’aikatar shari’a ta jihar ta yi bita ga masu rike da sarautun gargajiya 150 kan wayar da kan jama’a game da illar yi wa yara fyade a matsayin wani mataki na rage yawan fyade a fadin jihar.