Kwamati ya bankaxo badaqalar Naira biliyan 158 a Jigawa
Kwamitin bin diddigi da tantance ayyukan kwangila da gwamnatin da ta gabata ta gudanar a Jihar Jigawa da Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar ya kafa ya miqa rahotonsa, inda ya gano an yi badaqalar Naira biliyan 158 a jihar.Kwamitin a qarqashin jagorancin Alhaji Bello Mahmud ya xauki kimanin wata bakwai yana gudanar da aikinsa, kuma ya […]
Kwamitin bin diddigi da tantance ayyukan kwangila da gwamnatin da ta gabata ta gudanar a Jihar Jigawa da Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar ya kafa ya miqa rahotonsa, inda ya gano an yi badaqalar Naira biliyan 158 a jihar.
Kwamitin a qarqashin jagorancin Alhaji Bello Mahmud ya xauki kimanin wata bakwai yana gudanar da aikinsa, kuma ya yi zargin cewa an yi aringizo a kuxaxen kwangiloli tare da gudanar da ayyuka marasa inganci a zamanin gwamnatin Sule Lamixo.
Alhaji Bello Mahmud ya ce sun bankaxo ana bin jihar bashin Naira biliyan 158 da manyan ’yan kwangila suke bin gwamnatin baya.
Ya ce sun samu ayyukan kwangila barkatai har guda 265 da gwamnatin baya ta bayar kuma ba ta biya ba yayin da dama daga ciki ayyukan marasa inganci ne wasu ma an fara su an kasa kammala su
Ya qara da cewa sun kuma gano qananan ayyuka da aka ba qananan ’yan kwangila 465 a faxin jihar da ba a kammala wasu ba.
Shugaban kwamitin ya roqi Gwamna Badaru ya taimaka ya biya qananan ’yan kwangila bashin ayyukan da suka yi wa gwamnatin baya domin su samu damar ci gaba da yin wasu ayyukan.
Da yake mayar da jawabi bayan amsar rahoton kwamitin, Gwamna Badaru Abubakar ya gode wa ’yan kwamitin saboda qoqarin da suka yi wajen bankaxo badaqalar da tsohuwar gwamnatin ta binne a baya.
Ya ce kwamitin ya taka rawar gani, inda ya ce Majalisar Zartawa ta Jihar za ta duba rahoton da idon basira tare da xaukar matakin da ya dace a kai.