Kwamatin Sasantawa na PDP ya ziyarci Jigawa
‘Yan kwamatin sasanta tsakanin wadanda aka batawa da wadanda suke rike da ragamar jagorancin jam’iyyar PDP a jahar Jigawa sun ziyarci jahar domin dinke barakar dake tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar a kokarin da uwar jam’iyyar ta kasa key i na tabbatar da daidaito da a cikin jam’iyyar. Kwamatin ya sami zama da shugaban jam’iyyar na jahar […]

‘Yan kwamatin sasanta tsakanin wadanda aka batawa da wadanda suke rike da ragamar jagorancin jam’iyyar PDP a jahar Jigawa sun ziyarci jahar domin dinke barakar dake tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar a kokarin da uwar jam’iyyar ta kasa key i na tabbatar da daidaito da a cikin jam’iyyar.
Kwamatin ya sami zama da shugaban jam’iyyar na jahar Jigawa, Alhaji Salisu Mamuda Kuit a ofishin jam’iyyar a ranar Asabar da ta gabata a Dutse karkashin kulawar Alhaji Aminu Wali da Matawallan Maradun da kuma sauran ‘yan tawagar.
Kamar yadda bincike ya nuna, an bayyana cewa wai wani jigo ne a cikin jam’iyyar ya kai kara cewar ba a tafiya da shi a jam’iyyar a aikace, inda ya yi korafin cewar ba a yin komai da shi.
Amma shugaban jam’iyyar na Jahar jigawa, Alhaji Salisu Mamuda ya karyata waccan jita-jita, yana mai cewa su kansu a hade yake babu wadda aka bata da shi, a iya saninsu duk dan PDP yana cikin jam’iyyar.