Kwamishina ya bukaci kamfanonin sadarwa su tallafa wa ilimi

Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano AlhajiTajuddeen Gambo ya bukaci kamfanonin sadarwa da ke kasar nan su kara kokari wajen tallafa wa fannin ilimi ta yadda za su bada gudunmawa wajen bunkasa koyo da koyarwa a manya da kananan makarantun sakandaren kasar nan. Alhaji Tajuddeen Gambo ya bayyana haka ne jawabinsa wajen bikin bada kyaututtuka ga […]

Kwamishina ya bukaci kamfanonin sadarwa su tallafa wa ilimi
Kwamishina ya bukaci kamfanonin sadarwa su tallafa wa ilimi

Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano AlhajiTajuddeen Gambo ya bukaci kamfanonin sadarwa da ke kasar nan su kara kokari wajen tallafa wa fannin ilimi ta yadda za su bada gudunmawa wajen bunkasa koyo da koyarwa a manya da kananan makarantun sakandaren kasar nan.

Alhaji Tajuddeen Gambo ya bayyana haka ne jawabinsa wajen bikin bada kyaututtuka ga shugabannin makarantun Jihar Kano da malamai da kungiyoyi masu zaman kansu da kuma daidaikun mutane da aka zaba wadanda suke tallafa wa ilimi da aka zakulo a fadin jihar.
Ya ce idan kamfanonin sadarwa suna tallafa wa ilimi, ko shakka babu kwalliya za ta biya kudin sabulu ta fuskar ci gaban kasa da kuma al’umma musamman ganin cewa ilimi shi ne gishirin rayuwa ga kowane dan Adam.
Sai ya yaba wa dukkan wadanda suka samu kyaututtuka saboda kokarin da suke yi wajen bunkasa ilimi a Jihar Kano, a cewarsa aikin bunkasa ilimi yana bukatar hada hannu da gwamnati da masu kishin ganin al’umma sun samu ingantaccen ilimi tun daga tushe.
Ya ce gwamnatin jihar ta yi kokari kwarai wajen ba fannin ilimi kulawa ta musamman, wanda hakan ya sanya ilimi yake samun ci gaba a yankunan karkara da birane.
Alhaji Gambo ya nanata cewa za a ci gaba da gudanar da wannan biki na bada kyaututtuka ga hazikan shugabannin makarantu da malamai da kungiyoyin talafa wa ilimi da kuma daidaikun mutane da ke bada gudunmawarsu ga ci gaban ilimi duk shekara domin karfafa musu gwiwa.
daya daga cikin shugabannin makarantun da suka samu lambar yabo, kuma shugabar Makarantar Sakandaren ’Yan mata ta Arabiyya ta Dambatta, Hajiya Lauratu Ado diso ta ce wannan karramawa da aka yi mata ta kara mata kwarin gwiwar dada bada himma wajen inganta aikin koyo da koyarwa a makarantarta da kuma duk inda ta samu kanta.
Sai ta jinjina wa Kwamishinan ilimin da Babban Daraktan Hukumar Kula da Makarantun Sakandare ta Jihar Kano Alhaji Habib El-Yakub saboda kokarin da suke yi na bunkasa ilimi da kyautata yanayin koyo da koyarwa a fadin jihar ba tare da nuna gajiyawa ba.