Kwamishina ya rasu bayan fitowa daga taro da Gwamnan Kuros Riba
Ana tsaka da taron majalisar zartarwa ajali ya kira Abubakar Ewa, wanda shi ne Kwamishinan Yawon Buɗe Ido da Raya Al’adu na Jihar
Kwamishinan Yawon Buɗe Ido da Raya Al’adun Jihar Kuros Riba, Abubakar Ewa, ya rasu jim kaɗan bayan fitowarsa daga taro a fadar gwamnati.
Kwamishinan Yaɗa Labarai, Erasmus Ekpang, ne ya sanar da haka ta wayar tarho ga Wakikinmu.
Ya bayyana cewa su da gwamnan jihar suna tsaka da “halartar taron Majalisar Zartaswa ta Jihar, sa muka ga ya yi wa gwamna magana a kunne, wata kila yana neman izinin fita ne. Daga bisani muka ga ya fita, ya cewa kansa na ciwo.
“Bayan mun fito mun kakkarɓi wayoyinmu sai na ga kiraye-kiraye daga hadiminsa, watakila yana so ya sanar da ni abin da ke faruwa. Da na kira shi sai aka sanar da shi cewa an garzaya da Alhaji Abubakar Asibiti, inda a can rai ya yi halinsa.”
- An kai hari Fadar Shugaban Ƙasar Chadi
- Gwamnan Bauchi ya miƙa yaran da aka sace ga iyayensu
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Samun Wadataccen Abinci
Ekpang ya ce da jin haka duk ’yan majalisar zartarwar jihar suka garzaya zuwa asibitin domin tabbatarwa, “har yanzu muna cike da kaɗuwa.”
Honorabul Abubakar Ewa, wanda aka haifa a shekarar 1963 ya rasu yana da shekara 62.
Kafin zamansa Kwamishina ya ya zama Sakatare da kuma Shugaban Ƙaramar Hukumar Boki.
Kazalika ya riƙe muƙamin Darakta-Janar a zamanin mulkin tsohon gwamnan jihar, Ben Ayade.