Kwamishina ya tallafa wa iyalan mamatan ’yan sanda a Kano
A makon jiya ne Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano, Muhamamd Musa Katsina ya raba wa iyalan ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki kayan tallafi don kyautata rayuwarsu.Iyalan wadanda suka ci moriyar tallafin, sun hada da marigayi Sufeto Aliyu Usman da Saje Hassan Shu’aibu da Saje Bature Mamuda da Saje Mustapha Mustapha Idris da […]
A makon jiya ne Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano, Muhamamd Musa Katsina ya raba wa iyalan ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki kayan tallafi don kyautata rayuwarsu.
Iyalan wadanda suka ci moriyar tallafin, sun hada da marigayi Sufeto Aliyu Usman da Saje Hassan Shu’aibu da Saje Bature Mamuda da Saje Mustapha Mustapha Idris da Kofur Ahmad Garba da kuma Saje Joseph. Da yake raba kayan ga iyalan a madadin Kwamishinan, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, ASP Magaji Musa Majiya, ya ce kayayyakin da Kwamishina ya raba, sun fito ne daga aljihunsa.
“Tun lokacin da Kwamishinan ’ya zo Kano yake iya kokarinsa wajen kula tare da kyautata rayuwar jami’an wannan runduna. Da zarar an samu labarin rasuwar wani daga cikin ’yan sanda, zai yi umarni tare da bayar da abin tallafi ga iyalin mamacin nan take, “ inji shi.
A cewarsa Kwamishinan ya dauki aniyar bayar da irin wannan taimakon ne saboda imanin da yake da shi na cewa ta dalilin bayar da taimakon ne suke samun nasarorin tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin al’umma.
Majiya ya kara da cewa yana fata wannan abu da Kwamishinan ya yi zai zama abin koyi ga takwarorinsa na sauran jihohi, kuma ya zama wani abu da zai kara wa sauran ’yan sanda karfin gwiwar dagewa wajen gudanar da aikinsu da gaskiya.
Kayan da aka raba wa iyalan mamatan sun hada da buhunan shinkafa da katan-katan din taliya da yadiin shaddoji da atamfofi da Naira dubu 10 ga kowannensu. Malama Adama Ahmad Garba ta mika godiya ga Kwamsihinan ’Yan sandan, inda ta nuna cewa taimakon ya zo a daidai lokacin da ya dace.
“Muna godiya ga Kwamishinan ’Yan sanda bisa wannan taimako da ya ba mu, kasancewar taimakon ya zo a daidai lokacin da muke bukata. Kuma muna godiya ga sauran ’yan sanda bisa kulawar da suke ba mu tun daga lokacin da mazajenmu suka rasu,” inji ta.