Kwamishinan da ya yi wa Buhari fatan mutuwa ya rasu

Kwamishinan Raya Karkara da Jam’iyyun Gama-Kai na Jihar Benuwai da ake zargi da fatan mutuwa ga dan takarar Shugaban kasa Janar Muhammdu Buhari, Mista Aondowase Chia ya mutu. Mutuwar Mista Aondowase Chia ta jawo cece-kuce a harkokin siyasar Najeriya, bayan da aka ce ya yi ba’a cewa Janar Buhari yana daf da mutuwa, inda ya […]

Kwamishinan da ya yi wa Buhari fatan mutuwa ya rasu
Kwamishinan da ya yi wa Buhari fatan mutuwa ya rasu

Kwamishinan Raya Karkara da Jam’iyyun Gama-Kai na Jihar Benuwai da ake zargi da fatan mutuwa ga dan takarar Shugaban kasa Janar Muhammdu Buhari, Mista Aondowase Chia ya mutu.

Mutuwar Mista Aondowase Chia ta jawo cece-kuce a harkokin siyasar Najeriya, bayan da aka ce ya yi ba’a cewa Janar Buhari yana daf da mutuwa, inda ya ce, “saura kiris ya tafi,” yana nufin Buhari yana daf da shiga kabari.
A shekaranjiya Laraba ne Chia ya mutu yana da shekara 46, bayan ya gabatar wa majalisar jihar kasafin kudin ma’aikatarsa na bana a ranar Talatar da ta gabata ba tare da alamun rashin lafiya a tare da shi ba.
An ce lokacin da ya isa ofis a shekaranjiya Laraba, sai ya kasa tashi daga kujerarsa bayan ya zauna, inda aka gaggauta kai shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Benuwai da ke Makurdi inda ya cika. Ana da yakinin ya rasu ne sakamakon bugawar zuciya.
Mista Chia ya rasu ya bar mace daya da ’ya’ya takwas, kuma shi ne kwamishina na biyu a ma’aikatar da ya rasu a zamanin gwamnatin Cif Gabriel Suswam.
Wanda ya fara rasuwa shi ne Atorto Girgi da ya fito daga karamar Hukumar Ushong da ke jihar, kuma shi ma ya rasu ne yana cikin aiki shekara uku da suka gabata.
Shugaban Ma’aikata na Gwamnan, Farfesa Saint Gbilekaa, wanda ya jagoranci wakilan Majalisar Zartarwar Jihar don ta’aziyya ga iyalan mamacin a gidansa da ke Makurdi ya bayyana rasuwar a matsayin abin jimami.
An nada marigayin a matsayin Kwamishinan Matasa da Wasanni a shekarar 2011 kafin a mayar da shi Ma’aikatar Raya Karkara da Jam’iyyun Gama-Kai a shekarar 2013, inda yake har zuwa mutuwarsa.