Kwamishinan Lafiyan Legas ya kamu da COVID-19

Kamishinan Lafiya na Jihar Legas Farfesa Akin Abayomi ya kamu da cutar COVID-19

Kwamishinan Lafiyan Legas ya kamu da COVID-19

Kwamishinan Lafiya na Jihar Legas, Farfesa Akin Abayomi

Kamishinan Lafiya na Jihar Legas Farfesa Akin Abayomi ya kamu da cutar COVID-19.

Da safiyar Litinin ne Kamishinan Watsa Labaran Jihar ta Legas Gbenga Omotoso ya sanar da haka a safiyar Lahadi.

“Sakamakon kusanci da marasa lafiya da kuma kamuwarsa da cutar COVID-19, Kwamishinan Lafiya, Farfesa Akin Abayomi ya kamu da cutar. Farfesa Abayomi ya san hakan ne bayan gwajin da aka yi wa mutanen da suka yi mu’amala da masu cutar”, inji shi.

Zuwa yanzu mutun 17,894 ne a jihar Legas ke da cutar daga cikin 52,227 da Hukuma Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ta sanar.

Kwamishinan yada labaran ya ce ko da yake alamun cutar ba su bayyana a jikinsa ba, Farfesa Abayomi, “Zai killace kansa a gida na kwana 14 kamar yadda tsarin yake, amma zai ci gaba da gudanar da ayyuka daga kida”.

A kwanakin baya an yi ta rade-radin cewa ya kamu da cutar, kasancewarsa kan gaba a matsayin Mataimakin Shugaban Kwamitin Yaki da cutar a jihar, amma daga bisa gwamnatin jihar ta karyata.

Sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar ranar Litinin ta ce, “Muna masa addu’a tare da iyalansa a tsawon lokacin da zai kasance a killace”.