Kwamishinan ’yan sanda ya gargadi ’yan siyasan Jihar Oyo
Sabon Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Oyo Alhaji Muhammed Musa Katsina ya ja kunnen ‘yan takarar mukamai a zabe mai zuwa da magoya bayansu, da su guje wa yin kalaman da ka iya haifar da hargitsi. Kwamishinan ya yi wannan gargadi ne cikin jawabinsa a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga Gwamna Abiola […]
Sabon Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Oyo Alhaji Muhammed Musa Katsina ya ja kunnen ‘yan takarar mukamai a zabe mai zuwa da magoya bayansu, da su guje wa yin kalaman da ka iya haifar da hargitsi. Kwamishinan ya yi wannan gargadi ne cikin jawabinsa a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo
Ya ce babu dan siyasan da ya fi karfin a tsugunar da shi gaban shari’a ko mai girmansa. Ya ce a zamaninsa zai tabbatar da ganin rundunar ‘yan sanda a Jihar Oyo ta yi duk abin da za ta iya domin tabbatar da zaman lafiya da girmama dokokin kasa a jihar.
Kwamishinan ‘yan sanda Muhammed Musa Katsina, ya jinjina wa Gwamna Ajimobi a kan samar da zaman lafiya da yake kan yi, inda ya nemi iyaye da su tabbatar da sun ja kunnen ‘ya’yansu daga fadawa cikin rungutsumin siyasa, musamman irin yadda ake amfani da su a lokutan zabe da bayansa.
Ya ce rundunarsa a shirye take domin tabbatar da kare lafiya da dukiyoyin jama’a a Jihar Oyo. Saboda haka ya nemi hadin kan jama’a ta fannonin samar da labarai ga jami’ansa wanda zai taimaka wajen tabbatar da tsaro a jihar.
Da yake mayar da martani Gwamna Abiola Ajimobi ya yi maraba da sabon kwamishinan ‘yan sandan, wanda ya tabbatar masa irin rawar da ‘yan sanda suke takawa wajen tabbatar da tsaro, musamman ta fannin kafuwar runduna Operation, wacce ta bayar da gudunmawar tabbatar da tsaro a jihar. Ya yi fatan sabon kwamishinan da tawagarsa za su tabbatar da yin hobbasa, domin ganin an gudanar da zabe mai gabatowa lami lafiya a jihar.