Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Oyo ya nemi hadin kan Sarkin Hausawan a harkar tsaro
Sabon Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Oyo, Sola Sodipo, ya nemi hadin kan masarautar Sarkin Hausawan Ibadan, ta taimaka wajen shawo kan matsalar bambancin addini a tsakanin al’ummomi domin samun zaman lafiya mai dorewa. Haka kuma ya nemi Sarkin Hausawan Ibadan,, Alhaji Ahmad dahiru Zungeru, ya tashi tsaye wajen yin maganin miyagun mutane da ke aikata […]
Sabon Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Oyo, Sola Sodipo, ya nemi hadin kan masarautar Sarkin Hausawan Ibadan, ta taimaka wajen shawo kan matsalar bambancin addini a tsakanin al’ummomi domin samun zaman lafiya mai dorewa. Haka kuma ya nemi Sarkin Hausawan Ibadan,, Alhaji Ahmad dahiru Zungeru, ya tashi tsaye wajen yin maganin miyagun mutane da ke aikata laifuka su buya a masarautar domin tsira daga fadawa hannun jami’an tsaro.
Kwamishinan ‘yan sanda Sola Sodipo, ya yi wannan kira ne a ranar Alhamis ta makon jiya, lokacin da ya jagoranci wasu mataimakansa zuwa fadar Sarkin Hausawan Ibadan da ke unguwar Sabo domin gaisuwar ban girma.
Ya ce, a mahaifarsa mabiya addinan Musulunci da Kirista suna cakuda da juna ne ta fannin auratayya da makamantansu, kuma akwai wuraren ibada da suka hada da masallatai da coci coci da aka gina su a kurkusa da juna a mahaifar ta sa, inda a cewarsa za ka tarar da mabiyan addinin kirista suna taimaka wa musulmi da ruwan alwala da shimfidun sallah, su kuma Musulmi suna bayar da harabar masallatai ga kiristoci da suke gudanar da bukukuwansu a lokuta daban-daban.
“Irin haka ya kamata a rinka gani a ko’ina cikin kasar nan domin dukkanmu Allah daya muke bautawa,”inji shi.
Da yake mayar da martani Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ahmad dahiru Zungeru, ya tabbatar wa kwamishinan samun hadin kai da goyon baya, domin kyautata tsaro a wannan masarauta da Jihar Oyo da kasa baki daya.
Sarkin ya shaida wa kwamishinan cewa, “na samu hadin kan hakimai na wajen nada shugabannin kabilun Yarbawa da Ibo da Nufawa da Igala da suke zaune a cikin wannan masarauta, domin samun saukin shawo kan matsaloli da bankado miyagun mutane a cikinsu.”
Sarakunan Fulani da Barebari da Zabarmawa ‘yan kasar Nijar da Shugabannin Yarbawa da Ibo suna daga cikin manyan mutanen da suka halarci fadar domin sauraron jawabin sabon kwamishinan ‘yan sandan.
Kwamishinan ‘yan sandan yana tare ne da mataimakansa AC na Iyaganku Alhaji Bature Umar da AC Chris Owolabi da babban jami’in sashen binciken kwakwaf Anthony Okonkwo da kakakin rundunar ta jihar oyo Olabisi Okuwobi-Ilubanafor.