Kwamishinan ’Yan sandan Yobe ya bukaci matasa su tallafa wa tsaro
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Yobe Mista Markus K. danladi ya bukaci matasan jihar su fito a dama da su waken ba da gudunmawarsu a harkokin tsaro musamman ta ba da kariya ga al’ummominsu don karfafa gwiwar jami’an tsaron da ke yankunansu.Kwamishinan ya bayyana hakan ne ta bakin kakakinsa ASP Toyin Gbadegesin lokacin da yake zantawa […]
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Yobe Mista Markus K. danladi ya bukaci matasan jihar su fito a dama da su waken ba da gudunmawarsu a harkokin tsaro musamman ta ba da kariya ga al’ummominsu don karfafa gwiwar jami’an tsaron da ke yankunansu.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne ta bakin kakakinsa ASP Toyin Gbadegesin lokacin da yake zantawa da Aminiya a Damaturu.
Kwamishina ya ce, matasa na da muhimmiyar rawar takawa a harkokin da suka shafi tsaro ta wajen zage dantse don hada hannu da jami’an tsaro a fafutikar da ake yi na samar da ingantaccen yanayi na zaman lafiya.
Ya nemi shugabannin addini da na kungiyoyi su ci gaba da ba da gudunmawarsu wajen tabbatar da tsaro a jihar musamman wajen sa ido ga mutanen da ke shigowa cikinsu da sunan kama hayar gidaje.
Kuma ya shawarci al’umma su rika lura da irin mutanen da suke makwabtaka da su don kauce wa makwabtaka da baragurbi da ke shigewa cikin jama’a suna aikata ta’asa.
Ya ce da zarar sun gano bara-gurbin makwabci su hanzarta ba da rahoto ga hukumomin tsaro don daukar mataki a kai.
Kwamishin ya kuma bukaci direbobin motocin haya da na Keke NAPEP su rika lura da fasinjojin da ke shiga motocinsu ta wajen bincikarsu da kayayyakinsu kafi su shiga tasha don kauce wa masu kai harin kunar bakin wake.