Kwamishinar Mata ta gudu da manyan janaretocin gwamnati a Bauchi

Shugaban Kwamitin Karbo Kayayyakin Gwamnati daga jami’an tsohuwar gwamnatin Malam Isa Yuguda, Alhaji Tijjani Baba Gamawa ya nuna damuwarsa kan yadda tsohuwar Kwamishinan Ma’aikatar Mata Hajiya Talatu Muhammed Barwa ta yi awon gaba da manyan janaretocin gwamnati kirar GMT a lokacin da take rike da mukaminta. Alhaji Tijjani Baba ya ce Hajiya Talatu Barwa wadda […]

Kwamishinar Mata ta gudu da manyan janaretocin gwamnati a Bauchi
Kwamishinar Mata ta gudu da manyan janaretocin gwamnati a Bauchi

Shugaban Kwamitin Karbo Kayayyakin Gwamnati daga jami’an tsohuwar gwamnatin Malam Isa Yuguda, Alhaji Tijjani Baba Gamawa ya nuna damuwarsa kan yadda tsohuwar Kwamishinan Ma’aikatar Mata Hajiya Talatu Muhammed Barwa ta yi awon gaba da manyan janaretocin gwamnati kirar GMT a lokacin da take rike da mukaminta.

Alhaji Tijjani Baba ya ce Hajiya Talatu Barwa wadda ta rike mukamin Kwamishinan Ma’aikatar kananan Hukumomi ta Jihar kuma ta kula da Ma’aikatar Harkokin Mata, an ba ma’aikatunta manyan jannaretoci biyu amma sai ta gudu da su.
Ya ce: “Lokacin da muka samu labari mun je Ma’aikatar kananan Hukumomin muka bayyyana wa Babban Sakataren Ma’aikatar ya kira ta ya ba ta shawara ta dawo mana da janaretan gwamnati da ta yi awon gaba da shi.
Ya ce daga bisani ta kawo wasu tsofaffin janaretoci ba irin wadanda ta dauka ba, don haka suka sake ba ta shawarar ta dawo da janaretocin na ainihi.
Sai dai duk kokarin da wakilinmu ya yi domin jin ta bakin Hajiya Talatu Barwa kan wannan batu ya ci tura, inda ya kira wayarta a lokuta daban-daban ba ta shiga ba, har zuwa lokacin hada wannan rahoto.