Kwamishinoni 11 sun ajiye mukaminsu a Sakkwato
Mataimakin Gwamna da kwamishinan tsaro da na kudi sun yi murabus don fitowa takara a zaben 2023
Kwamishinoni 11 ciki har da Mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato sun mika wa Gwamna Aminu Tambuwal takardun ajiye mukamansu.
Kwamishinan tsaron jihar, da takwaransa na kudi da wasu mutum 12, ciki har da mataimakin gwamnan, sun ajiye kujerunsu na kwamishina ne domin fitowa takara a zaben 2023.
- NAJERIYA A YAU: Za A Kai Wa Wuraren Ibada Harin Bom —DSS
- Taimaka wa ’yan bindiga: An tsige sarakuna 2 da hakimi a Zamfara
Kazalika Sakataren Gwamnatin Sakkwato, Sa’idu Umar Ubandoma, ya ajiye mukaminsa tare da Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati, Mukhtar Umar Magori domin shiga zaben bayan su ma Gwamna Aminu Aminu Tambuwal ya amince da murabus dinsu.
Ga jerin Kwamishinonin da suka ajiye mukamansu sun ne:
- Kwamishinan Tsaro Garba Moyi.
- Kwamishinan Kudi, Bashir Gidado.
- Kwamishinan Addini, Abdullahi Maigwandu.
- Kwamishinan Ayyuka, Salihu Maidaji.
- Kwamishinan Muhalli, Sagir Bafarawa.
- Kwamishinan Kasa da Gidaje, Aminu Bala Bodinga.
- Kwamishinan Wasanni, Bashir Gorau.
- Kwamishinan Kudi, Abdussamad Dasuki.
- Kwamishinan Albarkatun Kasa, Abubakar Maikudi.
- Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Shu’aibu Gwanda Gobir.
- Kwamishinan Kananan Hukumomi, Mataimakin Gwamana, Manir Dan’iya.