Kwamiti ya biya wa fursunoni 15 tara a Bauchi

Kwamitin wa’azi da fadakar da jama’a na kungiyar Jama’atu Izalatul Bidi’a Wa Iƙamatus Sunnah ta kasa ta biya kudin tara ga fursunoni guda 15 da suke fuskantar zaman yari bisa laifuka daban-daban a gidan yarin Bauchi. Shugaban kwamitin na ƙasa, Malam Muhammad Malwan ya bayyana haka, a lokacin da suke gabatar da wa’azi ga fursunonin […]

Kwamiti ya biya wa fursunoni 15 tara a Bauchi

Kwamitin wa’azi da fadakar da jama’a na kungiyar Jama’atu Izalatul Bidi’a Wa Iƙamatus Sunnah ta kasa ta biya kudin tara ga fursunoni guda 15 da suke fuskantar zaman yari bisa laifuka daban-daban a gidan yarin Bauchi.

Shugaban kwamitin na ƙasa, Malam Muhammad Malwan ya bayyana haka, a lokacin da suke gabatar da wa’azi ga fursunonin da ake tsare da su a gidan yarin na Bauchi. Ya ce sun yi haka ne domin a ’yantar da fursinonin don su dawo cikin al’umma kuma su sami zarafin da za su ba da gudunmawa wajen ci gaba da gina ƙasa.

Ya ce: “Shiga gidan yari yana ƙara ilimi da basira da hangen nesa. A da wanda ba ya shigowa cikin gidan yari yakan ɗauki duk wanda ya samu kansa a gidan yari to mutumin banza ne, alhali kuma abun ba haka yake ba; domin wani laifinsa ne wani kuma jarabawa ce ta kawo shi ga shiga gidan yari, jarabawa ce da aka rubuta masa tun yana cikin mahaifiyarsa sai ya shiga gidan yari koda bai yi laifin komai ba.”

Malamin ya shawarci waɗanda aka ’yantar da su ji tsoron Allah, kada su koma aikata laifukan da suka kawo su ga shiga wannan gida. Ya kuma buƙaci jami’an gidan yarin da a kodayaushe su rika kyautata wa fursinonin da suke hannunsu tare kuma da ba su horo na musamman kan sana’o’in dogaro da kai domin bayan sun kammala wa’adinsu su samu abin yi.

Mataimakin shugaban gidan yarin, DC Sulaiman Inuwa ya nuna farin cikinsa bisa karamcin da ƙungiyar ta Izala ta yi wa fursunonin. Ya roki Allah Ya biya su da sakamako mai kyau. Ya ce an gina gidan yarin na Bauchi ne da nufin ya ɗauki mutum ɗari biyar kacal amma ya zuwa yanzu haka mutane sama da dubu ɗaya ne suke cikinsa. A kan haka ne ma ya yi kira ga masu hanu da shuni da su kawo ɗauki ta fuskokin da suka dace, kama daga biyan tara domin ’yanta wasu da kuma kawo tallafi kamar yadda ya dace, domin inganta ayyukan gidan yarin da kuma jin daɗin fursunonin.

Wasu daga cikin fursinonin da aka ’yantar sun nuna jin daɗinsu a bisa wannan karamci, inda suka sha alwashin cewa ba za su koma aikata ayyukansu na baya ba. Sun kuma yi fatan Allah Ya yafe masu laifukansu.