Kwamiti ya hakura da shaidar shugaban Ombatse

Mutumin da galibin jama’a suka hakkake shi ne shugaban addini na kungiyar Ombatse na al’ummar Eggon da ke Jihar Nasarawa da ake zargi da kashe jami’an tsaro 74, Baba Alkyo ya sake kin bayyana a gaban kwamitin binciken kisan na watan Mayu a kauyen Alakyo da ke kusa da Lafiya a ranar Litinin da ta […]

Kwamiti ya hakura da shaidar shugaban Ombatse

Mutumin da galibin jama’a suka hakkake shi ne shugaban addini na kungiyar Ombatse na al’ummar Eggon da ke Jihar Nasarawa da ake zargi da kashe jami’an tsaro 74, Baba Alkyo ya sake kin bayyana a gaban kwamitin binciken kisan na watan Mayu a kauyen Alakyo da ke kusa da Lafiya a ranar Litinin da ta gabata. Wannan ne karo na biyu da ya ki halartar zaman kwamitin, lamarin da ya sa kwamitin ya hakura da sauraron shaidarsa a lokacin da kwamitin ya sanar da shirinsa na kammala zaman.
Shugaban Kwamitin Mai shari’a Joseph Fola Gbadeyan mai ritaya ya ce, suna shirin kammala zaman kwamitin bayan sun yi zaman jiran Baba Alakyo na awanni ba tare da sun gan shi ba. Y ace kwamitin ya dage zamansa zuwa jiya Alhamis lokacin da zai amince da rubutattun jawabai daga lauyoyin da suka wakilci al’ummomi da kungiyoyi da daidaikun jama’a tun daga ranar 18 ga Yuli da ya fara zama a Lafiya.
’Yan sanda da jami’an tsaron kasa (SSS) na zargin mutumin da kungiyarsa da yin kwanton bauna tare da kashe musu jami’ai da dare a ranar 7 ga Mayu kuma suka kwace makamansu. Sai dai lauyan kungiyar Barista Zamani Zachary Allumaga ya musanta zarge-zargen. An shirya Baba Alakyo zai bayyana a gaban kwamitin a makon jiya amma ya ki, lamarin da ya tilsta kwamitin dage zamansa zuwa Litinin da ta gabata domin ya bayyana. Sai dai kuma bai bayyana ba, inda da misalin karfe 1:30 na rana sai lauyar kwamitin Misis Funso Lawal ta nemi a hakura da batun bayyanarsa.
Lauyan Gwamnatin Jihar Barista bon Jen ya goyi bayan bukatar, yayin da Barista Abdullahi Ubandoma da ke wakiltar Sarkin Lafiya da al’ummar Kwandare ya bukaci kwamitin ya dauka Baba Alakyo ya sarayar da ’yancinsa na ba shi damar kare kansa. Shi ma Barista Mohammed Elegu da ke wakiltar al’ummar Assakio ya amince da bukatar. Saboda haka shugaban kwamitin ya yanke shawarar hakura da batun sauraron shaidar Baba Alakyo kuma ya dage zaman kwamitin zuwa jiya Alhamis domin amincewa da rubutattun shaidu.
Kwamitin ya fadi a baya cewa Baba Alakyo zai bayyana ne bisa sharuddan da dattawan Eggon da sarkinsu Aren Eggon Dokta Bala Angbazo suka tsara. A makon jiya lauyan kungiyar Ombatse Barista Allumaga ya shaida wa Aminiya cewa Baba Alakyo ya kasa bayyana a gaban kwamitin ne saboda rashin tabbacin ba shi tsaro kamar yadda aka yi alkawari, ya ce mutumin ba zai bayyana ba saboda kungiyar ba ta san fasalin tsarin ba shi tsaron ba. Ya ce tun bayan dage zaman kwamitin na lokacin ba wanda ya sake tuntubarsu. Kuma ya yaba shawarar kwamitin na amincewa da rubutattun shaidun ba tare da jirar bayyanar Baba Alakyo ba. Kwamishinan Shari’a na Jihar Barista Lagi Innocent ya shaida wa Aminiya ta waya cewa gwamnatin jihar ta ba da tabbacin tsaro ga Baba Alakyo kamar yadda aka amince, inda ya ce sun yi alkawarin ba za su kama shi ba.