Kwamiti ya kona jabun kayayyaki na Naira miliyan 70 a Kano

Hukumar Kare Hakkin Masu Sayen Kaya reshen Jihar Kano ta kona jabu da gurbatattun kayayyakin da suka haura na Naira miliyan 70 da hukumar ta kama a cikin wata shida.An kone kayan a bainar jama’a a gefen wani kududdufi da ke Farawa a karamar Hukumar Kumbotso. Kayan sun hada da na bukatun yau da kullum […]

Kwamiti ya kona jabun kayayyaki na Naira miliyan 70 a Kano
Kwamiti ya kona jabun kayayyaki na Naira miliyan 70 a Kano

Hukumar Kare Hakkin Masu Sayen Kaya reshen Jihar Kano ta kona jabu da gurbatattun kayayyakin da suka haura na Naira miliyan 70 da hukumar ta kama a cikin wata shida.
An kone kayan a bainar jama’a a gefen wani kududdufi da ke Farawa a karamar Hukumar Kumbotso. Kayan sun hada da na bukatun yau da kullum da na abinci da sauransu.
A jawabinsa bayan kone kayayyakin, shugaban hukumar Alhaji Nuhu Bello, ya ce “Yau rana ce mai tarihi a lokacin mulkin Gwamna Rabi’u Kwankwaso, inda muka zo nan domin kone gurbatattu da jabun kayayyaki saboda kare lafiyar jama’ar Jihar Kano.”
Ya ce hukumarsu ta himmatu wajen kawar da sayar da gurbatattu da jabun kayayyaki ga jama’a, tare da wayar da kansu domin su kare matsayinsu a kasuwanni.
Ya ce masu sayen kaya a Najeriya suna cin karo da cututtuka daban-daban da masu sana’anta kayayyaki ko shigowa da su da dillancinsu suke jawowa.
Ya dangana faruwar hakan ga neman araha da jahilci na galibin masu sayen kayan, inda ya ce a shirye hukumarsa take ta kawar da wannan ta’asa domin kare rayuwar jama’a da lafiyarsu.
A jawabin wakilin Kwamishinan Kasuwanci, kuma Mataimakin Darakta a Ma’aikatar Kasuwanci ta Jihar, Alhaji Abdullahi Tafida, ya ce kone jabun kayayyakin ya nuna himmar gwamnati na kare jama’arta. Ya yi kira ga jama’a su rika sanar da hukumar kare hakkin masu sayen kaya, domin ci gaba da daukar mataki irin wannan.