Kwamiti ya kwato miyagun makamai a Jihar Kebbi

Kwamitin da Gwamnatin Jihar Kebbi ta kafa domin kula da tsaro a jihar, a karkashin jagorancin Mai ba Gwamnan Jihar Shawara kan Harkokin Tsaro Manjo Janar Muhammad Isah Dan Hanne (mai ritaya), ya samu nasarar kwato miyagun makamai daga masu garkuwa da mutane da ’yan fashi da makami. Kwamitin ya kwato makaman ne a yankunan […]

Kwamiti ya kwato miyagun makamai a Jihar Kebbi

Kwamitin da Gwamnatin Jihar Kebbi ta kafa domin kula da tsaro a jihar, a karkashin jagorancin Mai ba Gwamnan Jihar Shawara kan Harkokin Tsaro Manjo Janar Muhammad Isah Dan Hanne (mai ritaya), ya samu nasarar kwato miyagun makamai daga masu garkuwa da mutane da ’yan fashi da makami.

Kwamitin ya kwato makaman ne a yankunan kananan hukumomin Jega da Koko da Bagudo da Yawuri da Zuru da ke jihar.

Janar Muhammad D. Isah, ya bayyana wa Gwamnan Jihar Alhaji Abubakar Atiku Bagudu cewa sun yi amfani da dabarun tsaro wurin kama miyagun makaman.

Ya ce tallafin kudin da Gwamnatin Sanata Abubakar Atiku Bagudu ke ba kwamitin ne suke amfani wurin gudanar da ayyukan tsaro wanda hakan ya sa suka kai ga nasarar dakile aikata miyagun laifuffuka a jihar.

Ya ce kwamitinsa ya yi nasarar kama bindigogi kirar Pistol 25 da AK 47 2 da sauran bindigogi 68 da aka kama daga wadanda ake zargi da aikata miyagun laifuffuka a jihar.

Shugaban ya ce tuni wadansu daga cikin wadanda ake zargin suka mika wuya tare da mika makamansu ga kwamitin baya da suka ce sun tuba daga aikata laifuffuka.

Ya gode wa Gwamnatin Jihar Kebbi kan goyon bayan da take bai wa kwamitinsa domin gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

A jawabin Gwamna Abubakar  Atiku Bagudu ya bayyana jin dadinsa da godiya kan kwazon da kwamitin tsaro ke yi a jihar don tabbatar da cewa tsaro ya inganta a Jihar Kebbi. Ya ce wadannan miyagun makamai da aka kama ya nuna cewa mutanen jihar za su iya kwana idonsu rufe ba tare da tunanin wani abu ba.

Gwamnan ya kara da cewa aikin da kwamitin tsaro suka yi ba karamin aiki ba ne, kuma ya gode wa duk wadanda suka taimaka wurin tabbatar ta tsaro a jihar da kewayenta. Gwamnan ya ce Gwamnatin Jihar za ta ci gaba da ba kwamitin tsaro goyon bayan da ya dace domin kara inganta tsaro a jihar.