Kwamiti ya rufe gidajen mai da bankuna kan ba masu talla mafaka a Abuja

Kwamitin Musamman da Ministan Abuja Malam Muhammad Musa Bello ya kafa don magance cinkoson ababen hawa a kan titunan Abuja da kewaye, ya rufe gidajen mai biyu da wata kasuwar zamani(Plaza) da ke da bankuna biyu bissa zargin bada mafaka ga masu kasuwanci a gefen titi. Jagoran kwamitin Kwamared Attah Ikharo da ya samu rakiyar […]

Kwamiti ya rufe gidajen mai da bankuna kan ba masu talla mafaka a Abuja

Kwamitin Musamman da Ministan Abuja Malam Muhammad Musa Bello ya kafa don magance cinkoson ababen hawa a kan titunan Abuja da kewaye, ya rufe gidajen mai biyu da wata kasuwar zamani(Plaza) da ke da bankuna biyu bissa zargin bada mafaka ga masu kasuwanci a gefen titi.

Jagoran kwamitin Kwamared Attah Ikharo da ya samu rakiyar jami’an tsaro na hadin gwiwa a ranar Talata, ya ce kwamitinsa ya dauki matakin ne sakamakon yadda ake samun cinkoson ababen hawa a mashigar NNPC ta Kubwa inda harabobin gidajen man da kuma bankunan suke.

A zantawarsa da Aminiya ya ce matakin ya biyo bayan samun izinin daga Kotun Majistare ta Wuse Abuja ne, bayan shafe wata biyar suna neman masu wuraren da su hana kasuwancin bakin hanya a gaban harabobinsu da ya ce ke haddasa cinkoson ababen hawa musamman da safe da yamma.

Ya ce rufe wuraren zai ci gaba zuwa lokacin da masu su za su bi umarnin.

Yunkurin jin ta bakin masu wuraren da wakilinmu ya yi bai samu nasara ba har zuwa hada wannan  rahoto.