Kwamitin Amintattu na ACF ya yi watsi da dakatar da shugabansa

Kwamitin ya zargi tsohon babban sakatare na ƙungiyar, Murtala Aliyu, da haddasa rikicin bayan ƙarewar wa’adinsa.

Kwamitin Amintattu na ACF ya yi watsi da dakatar da shugabansa

Kwamitin Amintattu (BoT) na Ƙungiyar Arewa Consultative Forum, ya yi watsi da dakatarwar da aka ce an yi wa shugabansa, Alhaji Bashir Dalhatu, yana mai cewa matakin ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙungiyar kuma yunƙuri ne na haddasa rikici.

BoT ɗin ya bayyana cewa Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) ba shi da ikon dakatar da mambobin kwamitin amintattu, tare da zargin wasu tsirarun mambobi da shirya taron da ba bisa ƙa’ida ba domin sanar da dakatarwar.

Kwamitin ya kuma zargi tsohon babban sakatare na ƙungiyar, Murtala Aliyu, da haddasa rikicin bayan ƙarewar wa’adinsa, yana mai cewa duk matakan da ya ɗauka ba su da inganci.

Sanarwar, wadda manyan jiga-jigan Arewa suka sanya wa hannu, ta tabbatar da cewa ACF na nan cikin haɗin kai kuma za ta ci gaba da kare muradun Arewa.