Kwamitin Binciken Kisan Gillar Ombatse zai kai ziyara kauyen Lakyo
Kwamitin binciken kisan jami’an tsaro da ’yan kungiyar Ombatse suka yi a kauyen Lakyo da ke karamar Hukumar Lafiya a Jihar Nasarawa ya kafa kwamitin kwararru da zai je yankunan da rikicin kabilanci da rigirgimu suka shafa a jihar kwanakin baya don gano adadin barnar da aka yi. Shugaban kwamitin Mai shari’a Joseph Fola Gbadeyan […]

Kwamitin binciken kisan jami’an tsaro da ’yan kungiyar Ombatse suka yi a kauyen Lakyo da ke karamar Hukumar Lafiya a Jihar Nasarawa ya kafa kwamitin kwararru da zai je yankunan da rikicin kabilanci da rigirgimu suka shafa a jihar kwanakin baya don gano adadin barnar da aka yi.
Shugaban kwamitin Mai shari’a Joseph Fola Gbadeyan ne ya sanar da haka bayan zaman kwamitin inda ya ce “Kwamitin gani-da-idon da muka kafa mai dauke da kwararru, zai yi aiki ne a karkashin wannan kwamiti inda zai tafi kauyen Lakyo da wasu kauyukan da rikicin kabilancin ya shafa don gano adadin asarar da aka yi na dukiya da rayukan jama’a. Kuma bayan ya kammala ayyukansa zai mika rahotonsa ga kwamitin binciken domin daukar matakan da suka dace.”
A halin yanzu kwamitin na Mai shari’a Gbadeyan ya saurari koke-koke 22 daga wasu kauyukan da lamarin ya shafa da suka hada da Basa da Kadarko da Rutu da Kwandere da sauransu.
Sai dai lauyoyin al’ummar Eggon daga kauyen Lakyo inda ’yan Ombatse suka kashe jami’an tsaron da wasu kauyukan Eggon sun janye daga zaman kwamitin na Mai shari’a Gbadeyan.
Babban lauyan al’ummar Eggon Barista Zamani Zakariya Alumaga kuma mai magana da yawun bokan Ombatse ya sanar da haka a wata takardar bayan taro da lauyoyin Eggon suka rattaba wa hannu da aka raba wa manema labarai a Lafiya. Takardar ta ce lauyoyin sun dauki matakin janyewa daga halartar zaman kwamitin ne saboda ba ya gudanar da aikinsa yadda ya dace. Kuma bai ba lauyoyin isasshen lokaci don yin tambaya ga wadanda suke gabatar da koke-koke daga wasu kabilun.