Kwamitin Izala zai tallafa wa marayu 2,500 a Yobe

Kwamitin kula da marayu da matan da suka rasa mazajensu na kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah reshen Jihar Yobe zai raba kayan tallafi da suka shafi abinci da sutura ga gidaje 431 da ke dauke da marayu da matan da suka rasa mazajensu su 2,586 don rage musu wahalhalun da suke fuskanta musamman […]

Kwamitin Izala zai tallafa wa marayu 2,500 a Yobe
Kwamitin Izala zai tallafa wa marayu 2,500 a Yobe

Kwamitin kula da marayu da matan da suka rasa mazajensu na kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah reshen Jihar Yobe zai raba kayan tallafi da suka shafi abinci da sutura ga gidaje 431 da ke dauke da marayu da matan da suka rasa mazajensu su 2,586 don rage musu wahalhalun da suke fuskanta musamman a wannan wata na Ramadan.
Da yake jawabi a yayin nuna kayan ga Aminiya a Damaturu, shugaban kwamitin Alhaji Usman Mu’azu da mataimakinsa Malam Yusuf A. Muhammad ya wakilta ya ce, sun samu kayayyakin ne daga hannun al’umma bayan zagawa da ’yan kwamitin suka yi.
Ya ce, cikin kayayyakin da kwamitin ya raba akwai shinkafa buhu 20 da man girki da turamen atamfa 270 da bandur din yadin shadda 10 da takalman yara da na manya  da wasu kayan amfanin yau da kullum.
 Alhaji Usman Mu’azu ya ce wadanda suka ba kwamitin tallafin sun hada da Sakataren Gwamnatin Jihar Injiniya Baba Goni Machina da Farfesa Musa Alabi da shugaban karamar Hukumar Damaturu Alhaji Muhammad Kale da Hukumar SACA da Ma’aikatar Addini ta Jihar da daidaikun ma’aikata da ’yan kasuwa.
Tun farko shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Ustaz Ibrahim Muhammad Damaturu ya ce akwai jinsin mutum biyu masu rauni da Allah Ya ce a girmama su; matan da suka rasa mazajensu da yara marayu.
Don haka ya ja hankalin al’umma su rika taimaka wa marayu tunda Allah Ya ce, zai kusantar da duk wanda ke taimaka wa marayu tare da nisantar da su daga wutar Jahannama.
Ya yi nasiha ga maza da su rika auren matan da ke da nauyin ’ya’ya marayu su guji auren biyan bukatar jiki a rika duba maslaha ta addini. Ya ce sakamakon auren mata masu marayu Allah kan iya buda wa bawa hanyoyi masu yawa na ci gaban rayuwa da samun rahamar Ubangiji.
Ya gode wa ’yan kwamitin kan aiki tukuru har suka kai ga nasarar wannan aiki.