Kwamitin PCNI da Asusun bSF sun horar da ma’aikatan jaridun Intanet a Borno

A ranar 11zuwa 13 ga Disamba ne Kwamitin Shubaban kasa kan Farfado da Arewa maso Gabas (PCNI) da hadin gwiwar Asusun Tallafa wa wadanda rikici ya rutsa da su (bSF) suka gudanar da taron horarwa na wuni 3 ga ma’aikatan kafafen watsa labarai na Intanet su 40 a Jihar Borno. Taken taron shi ne: “Amfani […]

Kwamitin PCNI da Asusun bSF sun horar da ma’aikatan jaridun Intanet a Borno

A ranar 11zuwa 13 ga Disamba ne Kwamitin Shubaban kasa kan Farfado da Arewa maso Gabas (PCNI) da hadin gwiwar Asusun Tallafa wa wadanda rikici ya rutsa da su (bSF) suka gudanar da taron horarwa na wuni 3 ga ma’aikatan kafafen watsa labarai na Intanet su 40 a Jihar Borno. Taken taron shi ne: “Amfani da kafafen watsa labarai na Intanet don ayyukan jinkai da bayar da rahotannin ci gaba.” A lokacin bude taron, Mataimakin Shugaban Kwamitin PCNI da bSF, Alhaji Tijjani M. Tumsah ya ce an shirya horarwar ce domin a koyar da masu dauko rahotannin a kan yadda ya kamata su yi amfani da kafofin sadarwar zamani wajen bayar da labarai. Ya ce horarwa za ta taimaka wajen dawo da kyakkyawar fata da martaba da zaman lafiya da juna a tsakanin al’ummar yankin Arewa maso Gabas. 

Daraktar Asusun bSF, Farfesa Nana Tanko, ta ce za a shirya irin wannan horo a duk jihohin yankin shida domin inganta kwazon ma’aikatan kafofin labaran na Intanet tare da tabbatar da rahotannin da suke bayarwa sun karfafa fito da ayyukan jinkai a fili. A yayin rufe taron, mahalarta sun karbi takardun shaida kan kammala kwas din cikin nasara, kuma sun bayyana godiyarsu ga Kwamitin PCNI da Asusun bSF kan bullo da shirin.

Tarurruka na gaba za su gudana ne a jihohin Yobe da Adamawa kuma za a bayyana ranakun da za a gudanar da su a nan gaba