Kwamitin PCNI da Bankin Duniya sun shirya bita kan ayyukan farfadowa

A ranar 26 zuwa 28 ga Yuli ne Kwamitin PCNI da Bankin Duniya suka gudanar da taron bita na hadin gwiwa ga shugabanni da masu gudanar da shirye-shiryen ayyukan sake farfado da sassan da rikici ya shafa (MCRP).  Taron bitar na wuni uku, ya hado kan dukan masu ruwa-da-tsaki ciki har da gwamantocin jihohin Arewa […]

Kwamitin PCNI da Bankin Duniya sun shirya bita kan ayyukan farfadowa

A ranar 26 zuwa 28 ga Yuli ne Kwamitin PCNI da Bankin Duniya suka gudanar da taron bita na hadin gwiwa ga shugabanni da masu gudanar da shirye-shiryen ayyukan sake farfado da sassan da rikici ya shafa (MCRP). 

Taron bitar na wuni uku, ya hado kan dukan masu ruwa-da-tsaki ciki har da gwamantocin jihohin Arewa maso Gabas, don tsara ayyuka da hanyoyin da za su jagoranci aiwatar da ayyukan farfadowar da Bankin Duniya ke daukar nauyi.

An bullo da shirin ne bisa lura da mafiya muhimmanc da bukatun da ake son cimmawa a karkashin Shirin Buhari.