Kwamitin PCNI ya la’anci hari kan ma’aikatan Jami’ar Maiduguri da na Kamfanin NNPC
Shugaban Kwamitin Kwamitin Shugaban kasa kan Arewa maso Gabas Laftana Janar T.Y. danjuma ya yi Allah wadai da harin da ta’addancin da yawo mutuwar ma’aikatan Jami’ar Maiduguri da na Kamfanin Man Fetur na kasa (NNPC) da sojoji ciki har da wani hafsa da ’yan Sibiliyan JTF da suke yi musu rakiya don aikin gano man […]
Shugaban Kwamitin Kwamitin Shugaban kasa kan Arewa maso Gabas Laftana Janar T.Y. danjuma ya yi Allah wadai da harin da ta’addancin da yawo mutuwar ma’aikatan Jami’ar Maiduguri da na Kamfanin Man Fetur na kasa (NNPC) da sojoji ciki har da wani hafsa da ’yan Sibiliyan JTF da suke yi musu rakiya don aikin gano man fetur a kauyen Yesu da ke Magumeri a Jihar Borno.
Lamarin ya faru ne a ranar 25 ga watan Yuli bana. Janar T. Y. danjuma ya la’anci haka ne a sanarwa da ya fitar ta Kakakin Kwamitin PCNI, Alkasim Abdulkadir.
Ya yi ta’aziyya ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su da gwamnatin jihar inda ya yi addu’ar Allah Ya jikan mamatan.
“Mutuwar wadannan ’yan kishin kasa da aka kashe lokacin da suke aiki, ba ma mai daga hankali ba ne kawai, amma babban abin bakin ciki, asara ce mai muni ga mutanen jami’ar da kamfanin NNPC da sojoji da kuma ita kanta kasar nan.”