Kwamitin PCNI zai gudanar da taron wata-wata a karo na uku

Kwamitin Shugaban kasa kan Farfado da yankin Arewa maso Gabas (PCNI) zai gudanar da taron da ya saba yi wata-wata a karo na uku.  Taron zai gudana ne a ranar Talata 12 ga watan Satumba, 2017 a otel din Sandralia da ke Lamba 1 Titin Solomon Lar a Unguwar Utako (daura da Hedkwatar Hukumar Inshorar […]

Kwamitin PCNI zai gudanar da taron wata-wata a karo na uku

Kwamitin Shugaban kasa kan Farfado da yankin Arewa maso Gabas (PCNI) zai gudanar da taron da ya saba yi wata-wata a karo na uku.  Taron zai gudana ne a ranar Talata 12 ga watan Satumba, 2017 a otel din Sandralia da ke Lamba 1 Titin Solomon Lar a Unguwar Utako (daura da Hedkwatar Hukumar Inshorar Lafiya ta kasa, NHIS), Abuja.

Za a fara taron ne da misalin karfe 10 na safe. Taron zai ba damar tattauna abin da ya biyo bayan batutuwan da aka gabatar a taron baya.

Sannan zai bayar da dama mahalarta su tattauna kan kalubalen baya-bayan nan a Arewa maso Gabas da tsara hanyoyin shawo kansu da nasarar da abokan hadin gwiwa sua cimma da kuma tsara kasafin kudin badi da sauran batutuwa.

Za a karkasa taron daki-daki domin ba mahalarta damar su mayar da hankali kan zababbun yankunan da suka fi dacewa a mayar da hankali domin daddalewa tare da nemo mafita.