Kwamitin sake fasalin kasa na Arewa ya fara zamansa a Kaduna

Kwamitin Sake Fasalin Kasa na Kungiyar Gwamnanonin Arewa da  Sarakunan Gargajiya na yankin ya fara zamansa a jiya a jihar Kaduna. Taron wanda Shugaban Kwamitin, Gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Aminu Tambuwal ya jagoranta ya ce kwamitin zai tuntubi jama’ar yankin tare da sanya ra’ayoyinsu cikin kundin bayanan da kwamitin zai gabatar. Ya ce kwamitin nasu zai […]

Kwamitin sake fasalin kasa na Arewa ya fara zamansa a Kaduna

Kwamitin Sake Fasalin Kasa na Kungiyar Gwamnanonin Arewa da  Sarakunan Gargajiya na yankin ya fara zamansa a jiya a jihar Kaduna.
Taron wanda Shugaban Kwamitin, Gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Aminu Tambuwal ya jagoranta ya ce kwamitin zai tuntubi jama’ar yankin tare da sanya ra’ayoyinsu cikin kundin bayanan da kwamitin zai gabatar.
Ya ce kwamitin nasu zai yi amfani da garambawul din da Majalisar Dokoki take yi wa kundin dokokin Najeriya na shekarar 1999 inda za su duba yadda za su gabatar da ra’ayin baidaya da ya shafi yankin Arewa ga majalisar.
Wadanda suka halarci taron sun hada da Gwamnan jihar Nasarawa da na jihar Kaduna da na jihar Gombe wadanda membobi ne a kwamitin da kuma mataimakin gwamnan jihar Filato wanda shi ne sakateren kwamitin.
Sauran sun hada da Sarkin Kano da na Zazzau da Etsu Nufe na Neja da Gbong Gwom Jos da Sarkin Fika da kuma Sarkin Gumel.