Kwamitin wa’azin matasa na kungiyar Izala ya cika shekara biyu

Kwamitin wa’azin matasa na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) na Jihar Kuros Riba ya cika shekara biyu, kamar yadda shugabansa, Ustas Murtala Labbo Gusau ya bayyana, a yayin da yake zayyana wasu daga cikin irin nasarorin da kwamitin ya samu a cikin shekarun biyu da kafa shi. “Farko dai muna godiya ga […]

Kwamitin wa’azin matasa na kungiyar Izala ya cika shekara biyu

Ustaz Murtala Labbo GusauKwamitin wa’azin matasa na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) na Jihar Kuros Riba ya cika shekara biyu, kamar yadda shugabansa, Ustas Murtala Labbo Gusau ya bayyana, a yayin da yake zayyana wasu daga cikin irin nasarorin da kwamitin ya samu a cikin shekarun biyu da kafa shi.
“Farko dai muna godiya ga Allah da Ya ba mu dama muke shiga kowane sako na jihar nan don isar da sakon addinin Musulunci.  Kuma daga cikin nasarorin da wannan kwamiti ya samu, mafi girma shi ne samun musanyar bikin annashuwa da holewa, idan wani matashi ya yi aure, zuwa walima ta sunna, kamar yadda addinin Musulunci ya tsara”.
Ustas Labbo Gusau, ya shaida wa Aminiya haka ne a yayin da aka yi gangami wa’azin matasan a Kalaba, inda ya kara da cewa a halin yanzu kwamitin yana kokari ganin ’yan asalin jihar wadanda suka musulunta, musamman matasansu, ya dauki nauyin tura su karatu zuwa wasu makarantu domin su yi ilimi su san addini.  “Yin haka zai taimaka matuka wajen dabbakuwar addini a zukatansu kuma za su sami damar daukar nauyin gudanar da wa’azi a ko’ina a sassan jihar, musamman dayake su ’yan asalin jihar ne kuma sun san hali da yanayin zamantakewar mutanensu sosai fiye da baki.”  Inji shi.
Ya kara da cewa a duk yayin da suke gudanar da wa’azi ko yin duk wata mu’amala ta yau da kullum a tsakanin jama’a, suna iyakar kokarin ganin ba su nuna wa  kowa kyama ko kyara, suna nuna ’yan uwantaka ta mutumtaka don kaiwa ga manufarsu da yada dabi’un Musulunci.
A karshe shugaban ya bukaci ilahirin musulmi ko’ina suke su hada kai da juna domin haka shi zai magance irin tsargar da ake yi wa musulmi, musamman a wannan lokaci da kasar take cikin wani irin yanayi na rashin tabbas.