Kwamitin Wa’azin Matasa ya tallafa wa fursunoni a Jos
Kwamitin Wa’azin Matasa na kasa na kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ya kai wa fursunonin da ke babban gidan yarin garin Jos tallafin kayan masarufi a ranar Juma’ar da ta gabata. Kayan da kwamitin ya kai tallafi sun hada da madara da gari da sukari da sabulai da omo da kankana da abarba […]
Kwamitin Wa’azin Matasa na kasa na kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ya kai wa fursunonin da ke babban gidan yarin garin Jos tallafin kayan masarufi a ranar Juma’ar da ta gabata.
Kayan da kwamitin ya kai tallafi sun hada da madara da gari da sukari da sabulai da omo da kankana da abarba da sauransu.
Shugaban kwamitin, Malam Muhammad Murtala Idris Malwa ya bayyana cewa sun zo gidan yarin ne, domin su ga fursunonin su yi musu nasiha kan kyawawan halaye su kuma tallafa musu da kayan abinci saboda muhimmancin wannan wata na azumin Ramadan.
Ya ce wannan ziyara da suka kai gidan yarin na daya daga cikin ayyukan kwamitin da suka hada da ziyarar gidajen marayu da asibitoci domin tallafa wa marayu da marasa lafiya.
Shugaban ya ce suna gudanar da ayyukan gayya don gyara hanyoyi da makabartu da shirya wa matasa tarurrukan kara wa juna sani don kyautata rayuwarsu.
Ya yaba wa jami’an gidan yarin Jos kan yadda suke gudanar da ayyukansu na koyar da fursunonin tarbiyya tagari. Ya roki jami’an su rika ba kwamitin irin wannan dama a kowane lokaci, don ya rika zuwa yana gudanar da irin wannan aiki.
A jawabin Mataimakin Kwanturolan Gidan Yarin Jos Mista James Lander ya ce fursunonin suna bukatar taimako musamman a wannan lokaci na watan azumi. Ya ce a lokacin azumi gwamnati ba ta tanadar da wani abu ba don tallafa wa fursunonin, don haka akwai bukatar jama’a su rika tallafa musu.
Ya nuna rashin jin dadi kan yadda ake bari fursunoni a gidan yari shekara da shekaru ba tare da an kai su kotu ba.
Ya ce “Don haka a duk shekara muke rubuta wa gwamnati cewa ga wadanda suka dade a gidan yarin ba a yi musu shari’a ba, don haka ya kamata a sake su.”
Daga nan sai ya ce ba sa wasa da harkokin addini a gidan yarin domin addini na koyar da halaye masu kyau. “Don haka akwai masallaci da coci a gidan yarin da fursunonin suke gudanar da ibadarsu a ciki,” inji shi.
Ya yaba wa kwamitin kan ziyara da taimakon da ya kai, inda ya yi kira ga sauran kungiyoyi da ke Jos, su yi koyi da kwamitin wajen ziyartar gidan don ganin irin ayyukan da ake gudanarwa.
A jawabin shugaban fursunonin Malam Isiyaku Salihu ya yaba wa kungiyar Izala kan yadda take taimaka wa fursunonin gidan yarin na Jos. Ya ce a kwanakin baya kungiyar ta zo ta biya wa fursunoni 10 tarar da aka yi musu ta fitar da su daga gidan.