Kwamitin yakin zaben Buhari ya koka da Gwamnatin APC

Amma muna tabbatar da cewa har yanzu muna nan tare da Shugaba Buhari.

Kwamitin yakin zaben Buhari ya koka da Gwamnatin APC

Shugaba Buhari yana mika wa Ize-Iyamu tutar takarar jam’iyyar APC

Kwamitin yakin zaben Buhari a sashen Kudu maso Yamma (BCO) ya yi korafi a kan rashin samun ladan aiki daga Gwamnatin APC da ta cika shekara 6 tana mulki.

“A maimakon haka sai zargin mu ake yi da karbar miliyoyin kudi da kwangiloli da mukamai,” inji mutumin da ya jagoranci kafa wannan kwamiti, Sarkin Kudun Yamma Alhaji Hassan Isyaku.

Ya yi wannan karin haske tare da kare kwamitin daga wannan zargi a wajen wani taro da shugabannin rassan jihohi 6 na Kudu maso Yamma suka halarta a Ibadan.

Alhaji Hassan Isyaku ya ce ‘duk da yake ba mu samu komai ta fannin kwangila da mukamai da tallafin kudi a matsayin ladan aiki daga Gwamnatin mu ta APC ba, sai fama da kanmu, amma muna tabbatar da cewa har yanzu muna nan tare da Shugaba Buhari kuma za mu ci gaba da taimaka wa Gwamnatinsa.

Saboda haka muke yin kira ga wannan gwamnati mai adalci ta tuna da irin aikin da muka yi da wahalolin da muka fuskanta domin mu tabbatar da cewa mu ma ’ya’yan gwamnati ne masu goyon bayan ta.

A kan batun tsaron kasa, Sarkin Kudun Yamma Alhaji Hassan Isyaku ya yi kira ne ga al’ummar Arewa da ke zaune a wannan sashe da su ci gaba da hakuri da kyautata zamantakewarsu da jama’ar gari (Yarbawa) a jihohin da suke zaune domin hadin kan da zai taimaka wajen dakile mummunan nufin makiya Najeriya da ke son wargaza kasar.

Shi kuwa Sarkin ’yan gwangwan na Jihar Yamma Ambasada Ibrahim Abdullahi Soja da ya wakilci Jihar Legas a wajen taron cewa ya yi, “Mun sadaukar da rayuka da dukiyarmu wajen yi wa jam’iyarmu ta APC aikin da ya kai ga nasarar da ta samu na lashe zaben kasa baki daya a zangon farko da na biyu, amma har yanzu ba mu ga sakamakon aikin da muka yi ba.

A maimakon haka ma sai zargin mu ake yi da karbar miliyoyin kudi da kwangiloli daga hannun Gwamnatin alhali ko kwabo ba mu karba ba. Saboda haka muka fito mu karyata wannan zargi da kare kanmu.”

Ita ma wakiliyar Jihar Oyo a wajen taron, Hajiya Aminat Oparemi ta yi irin wannan korafi ne ga mahalarta taron da ta nemi kowanne ya koma jiharsa dauke da wannan sako ga daruruwan mambobin Kwamitin.

Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Osun Mista Wale Afolabi da fitaccen dan siyasa a Jihar Ekiti Alhaji Husaini Bawa da wakilan jihohin Ogun da Ondo suna daga cikin mahalarta taron.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50