Kwamitin Zakka ya raba sama da buhu 1800 a Jihar Sakkwato
Shugaban Kwamitin Zakka da Wakafi na Jihar Sakkwato Alhaji Lawal Maidoki ya ce kwamitin ya raba zakkar kudi da ta haura Naira miliyan daya da buhu 1,844 da tumaki da awaki 240 da shanu 42 da rakuma biyu da kuma damen hatsi dubu 14 a bara.Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Talata lokacin taron […]
Shugaban Kwamitin Zakka da Wakafi na Jihar Sakkwato Alhaji Lawal Maidoki ya ce kwamitin ya raba zakkar kudi da ta haura Naira miliyan daya da buhu 1,844 da tumaki da awaki 240 da shanu 42 da rakuma biyu da kuma damen hatsi dubu 14 a bara.
Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Talata lokacin taron soma fadakarwa kan sha’anin tara zakka da wakafi na bana a gundumomi 85 na jihar da aka yi a gundumar Tudun Wada.
Shugaban ya ce sun shirya fadakarwar ce saboda nan da wata biyu za su soma fara raba zakkar bana, don haka ya yi kira ga wadanda za su jagoranci kananan kwamitocin zakka a gundumomi su sanya tsoron Allah cikin wannan aiki domin samun nasara.
“Muna kira ga masu hannu da shuni su kawo wa kwamitin zakka ko wakafi, sa’annan ’yan siyasa su sani wannan kwamiti ba na siyasa ba ne, ko yin raraka ga wani,” inji Maidoki.