Kwamitinmu na taimakon marasa galihu 200 kowane wata – Maidoki

Malam Lawal Maidoki shi ne shugaban kwamitin Zakka da Wakafi na Jihar Sakkwato kuma shugaban kungiyar Matasa Musulmi ta Najeriya. Aminiya ta zanta da shi kan kwamitinsa don sanin ayyukansa da nasarori da matsalolin da yake fuskanta: Aminiya: Mene ne makasudin kafa Kwamitin Zakka da Wakafi na Jihar Sakkwato?Lawal Maidoki: Kwamitin Zakka da Wakafi a […]

Kwamitinmu na taimakon marasa galihu 200 kowane wata – Maidoki
Kwamitinmu na taimakon marasa galihu 200 kowane wata – Maidoki

Malam Lawal Maidoki shi ne shugaban kwamitin Zakka da Wakafi na Jihar Sakkwato kuma shugaban kungiyar Matasa Musulmi ta Najeriya. Aminiya ta zanta da shi kan kwamitinsa don sanin ayyukansa da nasarori da matsalolin da yake fuskanta:

Aminiya: Mene ne makasudin kafa Kwamitin Zakka da Wakafi na Jihar Sakkwato?
Lawal Maidoki: Kwamitin Zakka da Wakafi a da sunansa Kwamitin Sadaka, kuma Gwamna Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko ne ya canja masa suna zuwa na yanzu. Makasudin kafa kwamitin shi ne karbar Zakkah a rarraba ta domin kawar da talauci a tsakanin al’umma.  An fito da shirye-shiryen rage radadin talauci amma kwaliya ba ta biya kudin sabulu ba, saboda an bar tsarin Zakka da Wakafi da Allah da Ya tsara.
Idan tsarin da kwamitin yake bi ya dore za a samu zaman lafiya da walwala domin duk in da ake bin tsarin Allah kwanciyarhankali na mamaye wurin. Samar da soyayya tsakanin talakawa da mawadata na daga cikin abin da wannan kwamiti ke kokarin yi. Misali a zamanin Sayyidana Umar ya ce ba zai zartar da hukuncin yanke hannun barawo ba matukar ba a cikin wadata.
Muna wakiltar Gwamna ga biyan musakai kudinsu na tallafin wata-wata, muna biyan musakai 6923, kowane mutum daya mukan ba shi Naira 6,500. Muna bayar da tallafi ga marasa lafiya musamman na maganin da aka rubuto masu suka kasa biya, bayan mun yi binciken kwakwaf sai mu umurce shi ya karbi magani a asibiti ko dakin magani da muke a jiye kudi, kamarZumunci da Binji da sauransu.  A kowane wata kwamitinmu na ware Naira miliyan biyu domin taimaka wa marayu da marasa galihu 200, sannan a kowane wata muna ware Naira miliyan daya da rabi don taimaka wa wadanda ake bi bashi suka kasa biya saboda rashin hali. Haka masu son aurar da ’ya’yansu mata amma rashin kudi ya kawo musu cikas. Wadanda ginnisu ya fadi ko rufinsa ya kware muna taimaka musu. Kuma wannan kwamitin yana daukar nauyi wadanda tabin hankali ya shafa ta kai su asibitinmu a dauki nauyinsu har su warke. Wannan kwamiti na kafa mutum ta hanyar sana’a, ma’ana mukan ba da jari ga kananan sana’o’in hannu teloli da ’yan kasuwa da sauran sana’o’i. A yanzu haka a nan cibiyar muna horar da yara fiye da 120 kan yin takalma domin samar da ci gaba ga al’umma.
Kuma a kowane wata mukan ware Naira miliyan bakwai domin sayen abinci wanda muke son in Ramadan ya zo mu raba, wannan kadan ne daga cikin ayukkan kwamitinmu.
A halin yanzu gundumomi 58 daga cikin 63 da muke da su a Jihar Sakkwato  sun kawo bayanin zakkarsu kuma mun samu nasarar raba ta a gundumomi 31.
Aminiya: Baya ga gwamnati ko akwai wata kungiya ko daidaikun jama’a da ke taimaka wa kwamitinku?
Lawal Maidoki: To mutane a kauyuka suna ba da Zakka ga kwamitin da ke kusa da su, amma a nan cikin birni mutane ba su ba da Zakka ga kwamitinmu. Duk taimakon da na jero muna yi ne daga tallafin da Gwamna Wamakko ke bayarwa a kowane wata, inda yakan ba mu Naira miliyan 31 da rabi, sai Naira miliyan 45 da dubu 800 da yake bayarwa a raba wa musakai.
Alhaji Arzika Tambuwal da wani darakta sun taba ba mu zakkarsu, sai wani bawan Allah da ya ce kada a fadi sunansa da wani malamin jami’a da wata baiwar Allah da wani Mukhtar da ya ba da wakafi.
Ba wasu tsayayyun mutane da ke ba da wakafi ko zakkarsu ga kwamitinmu a kowane wata, yadda ka sami ofishinmu cike da jama’a haka yake koyaushe, a kowane yini mukan karbi koken mutum 100 ko 200 har 500.
Mutnen da nake aiki da su ina matukar jinjina musu yadda suke yin aiki tun safe har dare, ga shi ba wannan aikin kawai suke yi ba, kawai wannan taimako ne.
Aminiya: Mutanen gari za su kalli kudin da kuke karba sama da Naira miliyan 70 a kowane wata aikinku ya kamata ya fito a fili fiye da haka, me za ka ce?
Lawal Maidoki: Aikinmu a bayyane yake, a kowane wata in za mu raba kudi a kananan kwamitocinmu sai mun kira manema labarai, don su shaidi asibitoci da dakunan maganin da muke hulda da su.
Asibitin danfodiyo da na tabin hankali da ke Kware ne duk wanda bai gamsu ba ya je asibitocin ya tambaya ko ya nemi marasa galihun ya ji ko mun yi musu wani abu ko a’a.
A makon jiya mun raba awaki hur-hudu ga mata tsofaffi don su yi kiwo, kuma mun raba wa teloli 350 kekuna, sai injin nika 350 ga mata da firiza 80.
A halin yanzu mun mayar da karfi ga kafa kananan masana’antu, saboda mun fahimci sun taimakon jama’a.
Aminiya: Ka ce Gwamna na ba da tallafi kowane wata ga musakai don su daina bara amma ga mabarata nan sun cika gari, ko kuna da matakin dauka kan haka?
Lawal Maidoki: Kwamitin Zakka da Wakafi bayarwa aka samu, ba mu da hurumin kamawa ko ladabtar da mutum, in abin mu tafi da kai bakin titi ne mu kama mabaraci ka je ka ce me ga ciyaman na Zakka da Wakafi, gudu zai yi ba zai zo wurina ba saboda sun san muna ba su tallafi a kowane wata. Kuma akwai wadanda ke korafi ba su cikin shirin, mun zauna da su mun ce su fada mana bukatunsu don warware musu ko su je ga hakiminsu ya ba su takarda mu sanya su cikin shirin. Wasu kuma abin da suka ce mana gaskiya barar nan ba su iya barin ta. Ka ga akwai wata yarinya mai ciwon ido tana bin hanya tana fadin ‘don Allah a taimaka min magani za a yi min,’ na ganta a wata majami’ar Kiristoci a titin Ahmadu Bello, na kira ta muka je ofishina don a yi mata magani ta ki zuwa. Da na sake ganinta tana baran na ce mata ta ji tsoron Allah don ga yadda muka yi da ita a nan take wani mutum ya ce ya santa a garin Gwadabawa take.
Akwai wani dan majalisa da ya ba ni labarin wata mai bara ya ce ta tagar dakinsa ya ji tana waya tana fadin ta aika da Naira dubu 37 kada a bar yaron nan shi kadai a hada shi da wani don kai kudin wurin ajiya. Duba ta samu kudi amma ba ta iya tafiya ta ja jari ta yi sana’a.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno