Kwana 10 babu wanda ya kamu da COVID-19 a Malaysia

An shafe kwana goma a jere babu wanda ya kara kamuwa da cutar coronavirus a kasar Malaysia. Darakta Janar na Hukumar Lafiyar kasar Noor Hisham ya tabbatar da haka ranar Litinin. “Mutum 38 ne sabbin wadanda suka kara kamuwa da cutar a kwanaki 10 da suka wuce,” a cewarsa. 26 sun dauko cutar ne daga […]

Kwana 10 babu wanda ya kamu da COVID-19 a Malaysia

Firai Ministan Malaysia Muhyiddin Yasssin

An shafe kwana goma a jere babu wanda ya kara kamuwa da cutar coronavirus a kasar Malaysia.

Darakta Janar na Hukumar Lafiyar kasar Noor Hisham ya tabbatar da haka ranar Litinin.

“Mutum 38 ne sabbin wadanda suka kara kamuwa da cutar a kwanaki 10 da suka wuce,” a cewarsa.

26 sun dauko cutar ne daga wasu kasashe, 6 kuma a cikin gida, sannan akwai ‘yan kasashen waje mutum 6.

Zuwa ranar Litinin mutum 115 ne cutar coronavirus ta kashe daga cikin mutum 7,857 da suka harbu da ita a kasar.

Daga cikinsu 6,404 sun warke yayin da ake ci gaba da jinyar wasu 1,338.

Kofin Duniya: Jamus ta lallasa Curaçao da ci 7 a wasan farko

Mahaifinmu ba shi da ciwon suga – Ɗan Janar Rabe

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai