Kwana 100 da rasuwar Mandela: Sako na musamman ga ’yan Afirika

Tafiya sannu-sannu, Nelson Mandela har ya cika kwanaki 100 da mutuwa. A yayin da ake alhinin rashinsa, marubuciya, mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, A’isha Usman Liman, [email protected] ta rubuto wannan tsokaci a matsayin sako na musamman ga al’ummar Afirika, musamman ma ga ’yan kasar Afirika Ta Kudu da Najeriya. Wane sako ne wannan? […]

Kwana 100 da rasuwar Mandela: Sako na musamman ga ’yan Afirika
Kwana 100 da rasuwar Mandela: Sako na musamman ga ’yan Afirika

Tafiya sannu-sannu, Nelson Mandela har ya cika kwanaki 100 da mutuwa. A yayin da ake alhinin rashinsa, marubuciya, mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, A’isha Usman Liman, [email protected] ta rubuto wannan tsokaci a matsayin sako na musamman ga al’ummar Afirika, musamman ma ga ’yan kasar Afirika Ta Kudu da Najeriya. Wane sako ne wannan? Mu karanta a tsanake, kamar haka:  
Babban rashi kam an riga an yi shi ga kasar Afirika Ta Kudu da Nahiyar Afirika da ma duniya baki daya.
Nelson Mandela ka ta fi ka bar ’yan uwa bakar fata cikin alhini da kewa da juyayi da rashin sanin anya ko za a sake wani kamar ka, ko ma khalifanka a bayanka?
Lallai wannan jan gwarzon namiji (Mandela), ba karamin aiki ya yi wa bakar fatar kasarsa ba da Nahiyar Afrika, da ma duniya baki daya.
Wannan jan aiki da jarunta da jajircewa da ya nuna, shi ne ya yi musabbabin kai shi ga wannan babbar martaba da daukaka da ya samu a cikin duniya, wanda dukkan dan Adam yake muradin a ce shi ma ya samu irinta amma me ya yi masa sanadiyyar samun wannan daukaka?
Kamar yadda kowa ya sani, amsar a bayyane take kamar haka: Gaskiya, tausayi, rikon amana, fata ta gari ga kowa, hangen nesa, sanin ya kamata, hakuri, juriya, rashin ganin kyashi (rashin ganin fifiko), kai da duk wani hali nagari da mutun zai iya tunani da shi, to Mandela yana da shi kuma yana kamanta shi iya gwargwado kuma wadannan halaye nasa, su suka yi sanadiyyar sa shi sadaukar da rayuwarsa domin sama wa kasarsa da jama’arsa ’yanci da kwanciyar hankali.
Lalle kam Afirika Ta Kudu ba karamin rashi kuka yi ba, domin kun rasa mai son ku, mai kishin kasarku, mai yi muku fatan alheri a kodayaushe. Shi ya sa (mu ’yan Najeriya) muke taya ku juyayi da alhinin wannan babban rashi, domin mu ma mun san zafin irin wannan rashin na shugaba nagari irin Mandela.
Ku sani, wannan rashin idan ba sa’a kuka yi ba, kusan in ce kun yi shi ne na har abada. Ku da samun saukin ko daina kukan rashin Mandela sai illa masha Allahu, domin mu ma a can baya haka Allah Ya sa muka dace da shuwagabanni nakwarai, suka yi mana fafutukar samun  ’yanci, suka gina mana kasarmu cikin gaskiya da kishin kasa, suka shuka mana arziki kala-kala a kowane sako da lungu na kasarmu amma me zai faru? Tun ranar da Allah Ya sa kasa ta rufe fuskokinsu, har yau ba mu samu madadinsu ko in ce khalifansu ba. Kullum gwamma jiya da yau, haka kakanninmu suka shude suna alhinin rashin shuwagabanninmu nakwarai. Haka iyayenmu, har ga shi ya zo kanmu. Kullum idan an tashi tuna ’yan mazan jiya sai ka yi ta jin labarin jaruntaka da kishin zuci irin nasu, sai shauki da so da kaunarsu ya mamaye maka zuciya. To ga shi nan mu ma kusan haka za mu shude mu bar ’ya’ya da jikokinmu cikin irin wannan alhini da juyayi na rashin wadannan shuwagabanni nakwarai abin kauna, tun da har yanzu an rasa samun zakakuri ko zakakurai daga cikin shuwagabanninmu na yanzu, da zai yi hobbasa, ya cire son kai da kwadayin abin duniya,  ya raba mu da wannan gadadden kukan da muka kusan shekaru arba’in muna yi.
Yanzu kam kuma mai faruwa ta riga ta faru, Mandela dai ya riga ya koma  ga mahaliccinsa, sai dai mu ce don Allah ’yan Afirika Ta Kudu; kar ku bari wannan wahala da Mandela ya sha domin ku ta tafi a banza, domin kuwa duniya za ta zage ku, soboda da zarar kun ki bin tsare-tsarensa da manufofinsa da kudurorinsa da akidojinsa da ya bar ku a kansu, to kuwa kun dauko hanyar cin amanar Mandela kuma kun dauko hanyar koma baya da babu mafita a cikinta har abada.
Kuna dai ji kuna gani, koda Mandela ya shude yana fushi da shuwagabannin kasashe da dama, musamman ma na Nahiyar Afirika, ciki ko har da tamu kasar Najeriya, inda ya ce: “Koda a mafarki idan aka ce Najeriya za ta koma baya ta yi rashin dace da shuwagabanni irin wadanda muke da su a yanzu ba zan yarda ba.”
A cewarsa, Firaministan Najeriya na farko, Sa Abubakar Tafawa balewa ya taba ziyartarsa a kurkuku, ya karfafa masa gwiwa a kan fafutukar da yake yi wa kasarsa kuma ya ba shi kudi masu yawa (inji Dokta Hakim Baba Ahmed, a wata ziyara da ya kai wa Mandela a Afirika Ta Kudu).
Mu dai yanzu (’yan Najeriya) sai dai mu yi muku fatar alheri da fatar samun juriya da daidaito a cikin wannan hali da kuka tsinci kanku, na wannan babban rashin uban kasa, Mandela. Kuma Allah Ya nufe ku da samun natsuwa domin tsara dukkan manufofinsa da kudurorinsa da ya shinfida maku, yadda za ku ci gaba da cin moriyar su har abada.
Mu ma ’yan Najeriya, muna rokon Allah Ya kara tausaya mana, ya ganar da shuwagabanninmu su fahimci alfanun gaskiya da rikon amana da kishin kasa irin na shuwagabanninmu na farko.
Daga ’yar uwarku ’yar Afirika kuma mai fatar ganin dukkan kasashen Nahiyar Afirika sun samu adalan shuwagabanni ’yan kishin kasa kamar irin su Nelson Mandela.