Kwana 100 na Gwamnatin Buhari
Tabbas tun ran gini ran Zane, Hakika Shugaba Muhammadu Buhari kowa ya ga kamun ludayin Sabuwar Gwamnati. Domin tun daga ranar 29 ga Mayun da ka dare karagar mulkin kasarmu ta fara sauya alkibila daga hagu zuwa dama. Da farko da makwafta aka fara ziyar bangirma da nuna musu yanzu ba jiya ba ce. Ziyarar […]
Tabbas tun ran gini ran Zane, Hakika Shugaba Muhammadu Buhari kowa ya ga kamun ludayin Sabuwar Gwamnati. Domin tun daga ranar 29 ga Mayun da ka dare karagar mulkin kasarmu ta fara sauya alkibila daga hagu zuwa dama. Da farko da makwafta aka fara ziyar bangirma da nuna musu yanzu ba jiya ba ce. Ziyarar ka a Jamhuriyar Nijar da Kamaru da Chadi da Binin ta tabbatar da neman hadin kai da inganta tsaron nahiyarmu baki daya da habaka tattalin arzikin mu, uwa uba gayyatarka zuwa kasar Amuruka da taron G7. A kwana 100 nan wallahi har wutar lantarki ta canza. Domin kuwa babu ranar da ba a samun ta awa tara ba. Al’amarin yaki da rashawa ya zo karshe, duk Najeriya yanzu an san barayin kasa masu almundahana da dukiyar Najeriya. Lokaci kadan Shugaban ya ce mu ba shi don kwato wa al’umma dukiyar su, mun yi na’am da hakan. Domin ko rundunar tsaron kasa da ka yi wa kwaskwarima, yanzu sun san inda aka dosa da yaki da masu tada kayar baya, ba yaudara da karya a ciki. Muna addu’ar Allah ya taimaki Gwamnatin Muhammadu Buhari da kyakkyawar manufa ya haskaka mana kasarmu. Talakawa mu ci ribar romon dimokuradiyya. Daga Hafizu Balarabe Gusau 07035304499.