Kwana 7 na kasa barci saboda jiran hukuncin Kotun Koli —Bala Mohammed
Gwamna Bala ya yaba wa shugaban kasa Bola Tinubu kan rashin tsoma baki a harkokin shari’a
Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ya ce kwana bakwai ya kasa barci saboda jiran hukuncin Kotun Koli kan zabensa.
Bala Mohammed ya shaida wa magoya bayansa cewa, “Barci ya gagare ni ne saboda kullin da wasu tsofaffin shugabannin jihar suka je suka yi a fadar shugaban kasa da nufin a kwace kujerata.
“Sun shaida wa fadar shugaban kasa cewa ni matsala ne, kuma zan kara zame musu babbar matsala idan na ci gaba da zama Gwamna, amma cikin ikon Allah mun yi duk mai yiwuwa, kuma mun yi nasara a Kotun Koli.
“Sun je sun kulla makirci don shiga tsakanina da abokina, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, da ma shi kansa Shugaba Tinubu, duk da cewa yana yabawa da ayyukan da muka yi a jihar,” in ji shi.
- Abba ya nada Gawuna da Ganduje a Majalisar Dattawan Kano
- Kisan gilla: An fara binciken sojoji kan kashe Fulani 11 a Kaduna
Gwamna Bala ya yaba wa shugaban kasa Bola Tinubu kan rashin tsoma baki a harkokin shari’a, lamarin da ya haifar da hukuncin da aka yanke ranar Juma’a.
Ya kuma yaba wa Kotun koli bisa adalcinta ga dukkan kararrakin da aka shigar a gabanta, inda ya ce hukunce-hukuncen na ranar Juma’a sun dawo da martabar bangaren shari’a a matsayin matakin karshe na share hawayen talaka.
Daga nan sai ya ce yanzu abin da zai fi mayar da hankali a kai shi ne yi wa al’umma aiki tukuru da kuma samo wanda ya cancanta da zai maye gurbinsa, ya kuma yi wa al’umma aiki fiye da shi.