Kwana darin Buhari rahama ne ga Najeriya – Garba Maikwai

Shugaban Majalisar Dattawa masu burin Bunkasa Jihar Bauchi (Bauchi State Elders Promotion Council) shiyyar Bauchi ta Kudu Alhaji Garba Maikwai ya bayyana kwana 100 na gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin rahama ga al’ummar Najeriya.Alhaji Garba Maikwai ya bayyana haka ne lokacin da suke tattaunawa da wakilinmu a Bauchi a ranar Asabar da ta […]

Kwana darin Buhari rahama ne ga Najeriya – Garba Maikwai
Kwana darin Buhari rahama ne ga Najeriya – Garba Maikwai

Shugaban Majalisar Dattawa masu burin Bunkasa Jihar Bauchi (Bauchi State Elders Promotion Council) shiyyar Bauchi ta Kudu Alhaji Garba Maikwai ya bayyana kwana 100 na gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin rahama ga al’ummar Najeriya.
Alhaji Garba Maikwai ya bayyana haka ne lokacin da suke tattaunawa da wakilinmu a Bauchi a ranar Asabar da ta gabata, inda ya ce ba domin zuwa gwamnatin Buhari ba, kila da yanzu kasar nan ta rushe ko tana gab da rushewa.
Alhaji Garba Maikwai ya ce, kafin zuwan wannan gwamnati baya ga tabarbarewar tsaro an kai matsayin da albashi yana neman gagara a jihohi da kananan hukumomi da tarayya, inda ya ce da gwanmnatin tsohon Shugaban kasa Gooluck Jonathan ta zarce kananan hukumomin ana shirin rushe su kwata-kwata duk da cewa sun fi kusa da talakawa.
dan siyasar ya ce koda gwamnatin Buhari ba ta yi komai ba, yadda ta samu nasarar dawo da zaman lafiya a kasar nan tare da rage kaifin hare-haren bama-bamai da ayyukan ta’addanci a sassan kasar nan babban abin godiya ne da farin ciki.
Ya ce sannan an samu nasarar dakile yadda ake satar fitar hankali ga dukiyar kasar nan, ya ce dukiyar da ake kwatowa da wasu ke guna-gunin ana kwace kayan wasu kayan jama’a ne da suka sace ake kwatowa domina nuna musu abin da suka yi ba daidai ba ne. “Don haka wannan farfaganda ta neman bata sun aba za ta yi nasarar kawar da yaki da almundahanar da gwamnatin ta Buhari take yi don ceto kasar nan ba,” inji shi.
Ya kara da cewa: “Kada mu zamo masu gaggawa tare da nuna rashin gamsuwa kan irin tafiyar da gwamnatin Buhari take yi. Tafiyar da gwamnatinsa take yi shi ne abin da ya dace, domin gaggawa aikin Shaidan ne tana iya haifar da nadama da na-sani a nan gaba. Mutanen da Buhari ya fara nadawa a kan mukamai a yanzu mun hakkake mutane ne masu gaskiya da kishin kasa kuma alamu sun nuna cewa lallai za a yi zaman gaskiya a kasar nan.”
Sai ya bukaci jama’a su ci gaba da bai wa gwamnatin Buhari goyon baya da hadin kai, kuma ya roki gwamnonin jihohi da sauran shugabanni a dukkan matakai su yi koyi da Shugaban kasa Buhari wajen nuna shugabanci nagari da nuna gaskiya da rikon amana da fifita bukatun kasa da talakwa a kan bukatunsu domin ci gaban kasar nan.

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi