Kwanaki 100 na Shugaban kasa da gwamnoni: Ina aka dosa?

Yau ma mun ba da aron filinmu ga wani makarancinmu Alhaji  Shu’aibu Idris (Mikati) tsohon manaja a kamfanin Dangote, dan kasuwa kuma dan siyasa da ya taba neman tsayawa takarar Gwamnan Jihar Kaduna a Jam’iyyar PDP a zaben 2007. Ya yi tsokaci ne kan cika kwana 100 na gwamnatin Buhari da kuma gwamnonin kasar nan: […]

Kwanaki 100 na Shugaban kasa da gwamnoni: Ina aka dosa?
Kwanaki 100 na Shugaban kasa da gwamnoni: Ina aka dosa?

Yau ma mun ba da aron filinmu ga wani makarancinmu Alhaji  Shu’aibu Idris (Mikati) tsohon manaja a kamfanin Dangote, dan kasuwa kuma dan siyasa da ya taba neman tsayawa takarar Gwamnan Jihar Kaduna a Jam’iyyar PDP a zaben 2007. Ya yi tsokaci ne kan cika kwana 100 na gwamnatin Buhari da kuma gwamnonin kasar nan:

Mulkin dimokuradiyya ya fara samun gindin zama a Najeriya musamman da Allah Madaukakin Sarki Mai kowa da komai Ya sa muka samu yin zabe cikin lumana kuma bisa dukkan alamu wadanda aka zaba mutanen da jama’a ke so ne. Ma’ana kusan mu ce an bari zabin mutane ko abin da suke so shi ne aka ba su.
A gobe za mu cika kwanaki dari na ýfarko da kama mulkin Mai girma Shugaban kasa Muhammadu Buhari. A al’ada, akan yi biki don ciki wadannan kwanaki. A gaskiya kwanaki dari ba su da yawa kuma sun yi kadan, sun yi gajarta kuma lokaci ne takaitacce. Bai yiwuwa a ce za a yi wa mai mulki adalci ta duba aiki ko ayyukan da mai mulkin ya yi a cikin wannan karamin lokaci balle a ce za a gano ko yana da kokari ko ba ya da kokari.
Akan zabi shugabanni don su yi mulki na tsawon shekara ýhudu wato kwana 1,464. Idan aka ce za a dubi aikin da suka yi cikin kwanaki dari na farko don a yabe su ko a zage su ba zai yiwu a yi musu adalci ba. Ma’ana kwanaki dari ko mu ce wata uku daga cikin kwanakin da aka dibar musu wato kwana 1,464 ko mu ce shekara hudu ko kuma wata 48, hakika gajeren lokaci ne, musamman idan muka duba cewa kwanakin ko watannin ba su wuce kashi shida bisa dari na yawan kwanakin da masu mulkin za su yi ba. Wato kwana dari ko wata uku bai su kai ma kashi goma cikin dari na tsawon kwanaki ko watannin mulkin da aka diba wa mai mulkin ba ke nan.
Bayanin tsawon kwanaki dari na farko ya zama dole don jama’a su fahimci cewa idan za a yi wa masu mulki adalci to kada a yanke hukunci bisa matakan da suka dauka ko suka kasa dauka cikin wadannan kwanaki.
Idan muka dubi masu mulkin kuma za mu iya kasa su kashi biyu ko uku. Sababbin zababbun gwamnoni, akwai wadanda suka koma kan kujeransu wato za su maimaita shekara hudu ke nan, kamar su Alhaji Ibrahim Dankwambo na Jihar Gombe da Alhaji Umaru Al-Makura na Jihar Nasarawa,  akwai sababbin zaba wadanda suke a cikin jam’iyya daya da wanda suka gaje shi kamar su Alhaji Umar Ganduje na Kano da Alhaji Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sakkwato, akwai sababbin zababbun gwamnoni wadanda suka karbi mulki daga hannun wata jam’iyya, kamar su Malam Nasiru El-Rufa’i na Jihar Kaduna da Mista Samuel Ortom na Jihar Benuwai ýda sauransu.
A gaskiya yin tsokaci bisa ayyukan da kowannensu ya yi a cikin kwanaki dari na farkon mulkinsu dole ya sha bamban.
Wadanda suka kama mulki sabo sun sha bamban da masu maimaitawa. Haka nan wadanda suke jam’iyya daya da wadanda suka karba a hannunsu ya kamata su zama daban da wadanda ba jam’iyyarsu daya ba.
Wadanda suka shigo gwamnati daga gefe kamar Alhaji Badaru Abubakar na Jihar Jigawa da Musta Simon Lalong na Jihar Filato kamun ludayinsu zai sha bamban da na su Alhaji Atiku Bagudu na Jihar Kebbi da  Alhaji Abdullahi Ganduje da Alhaji Aminu Waziri Tambuwa wadanda suke cikin gwawnati da dadewa. Fahimtar gwamnati da yadda ake tafiyar da gwamnati zai sha bamban.
Mai girma Muhammadu Buhari Shugaýban kasarmu ya karbi mulki daga hannun Mai girma Dokta Goodluck Ebele Jonathan na Jam’iyyar PDP. Shugaba Buhari ya dade ba ya cikin gwabnati, saboda haka, hakika dole ne shigarsa cikin mulkin kasarmu sai yayi a hankali kuma ya natsu sosai don ya samu cikakkun bayanai don ya fahimci halin da kasa ke ciki. Idan bai natsu ya bi a hankali ba, aka yi komai cikin hanzari ko sauri ana iya samun matsaloli masu yawa.
Hakika Shugaba Buhari ya yi tunani mai zurfi da bai bari ’yan na-iya ko masu kukar cewa ya ki nada kowa a gwamnatinsa har an dauki dogon lokaýci. Aiki cikin gaggawa na tare da kure kuma aikin Shaidan. Kuma yakan jawo yin nadama! Allah Ya kyauta, amin.
Wasu daga cikin gwamnonin kamar su Alhaji Aminu Waziri Tambuwal Matawallen Sakkwato sun kamar irin wannan salo na Shugaban kasa wato jinkirta yin nade-nade ko bayar da mukamai.
Wanda duk ya yi niyyar yin ginin gidan sama dole ya yi fandisho mai kauri mai karfi. Kwanakin darin farko na sabon shugaba kamata ya yi su zama lokacin yin fandishan na yin mulkin adalci da biyan bukatun taýlakawan da suka zabi mai mulkin.
Idan muka dubi Shugaban kasa, a lokacin yakin neman zabe, ya yi alkawura da yawa. Ya yi alkawarin yaki da rashawa da cin hanci, ya yi alkawarin kawo karshen matsalolin tsaro da suka addabi kasarmu, ya yi alkawarin tallafa wa matasa da aiki don samun saukin talauci, ga fanonin ilimi da noma da wutar lantarki da hako ma’adanai ba a bar su baya ba, wajen daukar alkawuran duba su.
Ayyukan suna da yawa kuma an ci kwana dari ne kawai cikin kwanakin mulki da aka dibar masa wato kwana 1,464. Ashe ko cikin kwanaki dari na farko, sai dai a tsakuro daga cikin abubuwan da aka yi kudirin yi wa talakawa. Mai lura ko sharhi bisa abubuwan da aka samu yi cikin wadannan kwanaki sai ya yi taka-tsantsan don yin adalci.
Masu iya magana sun ce Juma’ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake ganewa! Hakika kuma ginshikin ginin, shi ne kan sa a tabbatar da cewa gini zai dore ko zai yi karko ko ba zai yi ba.
A cikin alkawura da akayi wa jama’a, bisa dukkan alamu, Shugaba Muhammadu Buhari ya tunkari yaki da rashawa da cin hanci wurjanjan. An kafa kwamitin ba da shawara a karkashin Farfesa Itsai Sagay sanannen mai kyamar cin hanci da masu cin hanci. An nada kwamiti ýdon ya duba sayo makaman yaki ga sojoji. Haka nan almundahanar da aka yi wajen rangwamen kudin man fetur da gwamnatin Dokta Jonathan ta kasa matsa wa wadanda suka ci kudin ko da tumbudi su yi idan ba su yi amai ko hararwa ba, an nada kwamitin binciken me ya faru. Hakika a bisa alkawarin yaki da rashawa da cin hanci da aka yi wa jama’a, an dauki matakan cika alkawarin. Sai dai mu yi ta addu’a Allah Ya kare kuma Ya kara ba da karfin gwiwar ci gaba don karbo hakkin talakawa daga wajen tsirarrun da suka yi rub-da-ciki a kan dukiyar jama’a.
An dade ana almubazzaranci da kudin kasa! barna, ko nuna halin ko oho da akan yi da dukiyar jama’a ta ragu. Kusan mu ce Najeriya da kuma jama’ar Najeriya musamman ma’aikatan gwamnati da ’yan siyasa an saka su cikin kurkukun idon Muhammadu Buhari. Mutane na tsorace kuma ana taka-tsantsan ba kamar da ba, da kowa yake yin abin da ya ga dama. Babu babba ba yaro, babu mai fada a ji! Mun zama kamar zaman kara-zube.
Bayanai sun gabata cewa an samu karin lokutan da jama’a ke samun wutar lantarki. Haka nan bisa dukkan alamu an fara daukar matakan farfadowa da inganta noma da hako ýma’adanai don samar wa matasa aikin yi da kuma yaki da talauci da rage dogaro da kasarmu ke yi a kan man fetur.
A fannin tsare-tsaren tattalin arziki kuwa, hakika Shugaban kasa na fuskantar matsanancin karancin kudi don yi wa talakawa aiki. Man fetur da muke sayarwa mu samu kudin shiga farashinsa ya fadi kasa warwas. Da ana sai da ganga daya kimanin Dalar Amurka 115 yau ya dawo Dala 47! Wannan ba karamin tashin hankali ba ne.
Matakin da Shugaban kasa ya dauka na dode duk hanyoyin almubazzaranci da barna da satar kudin jama’a sun fara yin tasiri. Tsawatawar da ya yi na a bude asusu guda daya na Gwamnatin Tarayya a Babban Bankin kasarmu don ajiye kudin jama’a daga baya a raba wa gwamnatoci ya yi tasiri kwarai da gaske. Wannan mataki ya nuna za a rika tafiyar da sha’anin tara kudin jama’a a fili ba a cikin sirri ba, da kuma yi musu cin mummuke. Kowa zai fahimci nawa aka tara kuma nawa za a  raba da yanayin rabon. Wannan mataki ya sa har darajar Naira ta fara dawowa. Kafin aiwatar da wannan tsari Dalar Amurka daya akan same ta a kan Naira 240, yanzu ta dawo Naira 207!
Hakika masana tattalin arzikin kasa da masu sha’awar zuba jari ko kafa masana’antu a Najeriya suna kokawa da jinkirin da ake samu kan fidda kudirin gwamnatin Buhari a bangaren tattalin arzikin kasa. Hakika ya kamata a hanzarta fidda kasida kan manufa da akidar wannan gwamnati karara don jama’a musamman masu hannu da shuni su fahimci inda gwamnati ta sa a gaba da kuma kudirorinta.
A karshe ina ganin ya kamata jama’a mu tashýi tsaye mu muke wajen addu’a, fatan alheri da ba da shawarwari ga shugabanninmu baki daya. Mu rage giba da zunde, mu daina zage -zage kuma mu kanne don gyara ba ya yiwuwa sai an ji zafi. Mu ne muka roki Allah Ya kawo mana canji, an samu canjin kuma da alamar canjin mai amfani ne. Bai kamata jama’a su dauki lafazin tsinuwa ko zagi ga shugabannimu ba idan an ga sun yi kuskure, mu nemi karin bayani, mu yi tambaya sannan mu hanzarta ba shugabannin urzi.
Allah Ya taimaka, amin.
Shu’aibu Idris Mikati
dan kasuwa ne kuma dan siyasa
Za a iya samunsa ta: [email protected]