Kwanaki kadan suka rage min a duniya – Rachael Bland ta BBC
Wata mai karanta labarai a shirin 5 Libe na gidan rediyon BBC da ke Landan, Rachel Bland, ta bayyana wa duniya a shafukan sada zumunta cewa sauran kwanaki kadan suka rage mata ta mutu. Likitoci sun gano ma’aikaciyar mai shekara 40 tana dauke da cutar daji a mamanta a watan Nuwamban 2016, kamar yadda gidan […]

Wata mai karanta labarai a shirin 5 Libe na gidan rediyon BBC da ke Landan, Rachel Bland, ta bayyana wa duniya a shafukan sada zumunta cewa sauran kwanaki kadan suka rage mata ta mutu.
Likitoci sun gano ma’aikaciyar mai shekara 40 tana dauke da cutar daji a mamanta a watan Nuwamban 2016, kamar yadda gidan rediyon BBC ya ruwaito.
Gidan rediyon ya ce a watan jiya ta ce tana sauri ta kammala rubuta wani littafi domin danta mai suna Freddie, kuma mai shekara biyu a duniya ya karanta bayan ya girma.
Ta ce ta tabbatar ba za ta shekara ba mutuwa za ta riske ta.
Baya ga karanta labarai, Rachel takan gabatar da shirin You, Me and the Big C, tare da Deborah James da kuma Lauren Mahon.
A ranar Litinin ce, ta aika da wani sakon Tiwita, inda ta ce abokan aikinta biyu za su ci gaba da gabatar da shirin bayan ta rasu.
Sakon ya ce: “Kamar yadda shahararren mawakin nan Frank S., ya ce: “Ina sanar da ku abokaina cewa lokacin ya karato. Kuma kwatsam ya iso. An sanar da ni cewa kwanaki kadan suka rage min. Abin tamkar mafarki. Ina mika godiyata gare ku saboda karfafa min gwiwa da kuka rika yi.”
An haifi Rachel a birnin Cardiff (Kadif), amma tana zaune ne a birnin Cheshire na kasar Ingila. A watan Mayun bana aka sanar da ita cewa babu magani ga cutar dajin da take fama da ita.
Amma bayan wata biyu sai bincike ya nuna wa likitoci cewa cutar ta kara bazuwa zuwa wasu sassan jikinta.
Abokiyar aikinta a shirin 5 Libe ta aika mata da sako, inda ta ce: “Kin zama mace mai ban al’ajabi gare ni. Ina mika kaunata ga kowa.”
Shi ma abokin aikinta, Tony Libesey wanda ke gabarta da shirin 5 Libe Dribe ya aike mata da sako a shafinsa na Tiwita: “Wannan irin karfin zuciya da kike da shi. Jinjina ga matar da ta fara nuna min yadda aiki yake a @bbc5libe, ina so ta sani cewa muna tare da ita a daidai wannan lokaci.”
Sauran abokan aikinta da masu sauraro ma ba a bar su a baya ba, inda suka aike mata da sakonnin karfafa gwiwa da jinjina.