Kwanakin karshe (1)

Lokaci ya gabato da ba sai an tunatar da mu ba a kan abubuwan da suke faruwa da mu a duniyar nan dare da rana. Muna gani muna kuma jin abubuwan ban mamaki da suke faruwa a ko’ina a fadin duniyar nan. Kowace rana tana dauke da nata labari, wayewar kowace safiya za ka ji […]

Kwanakin karshe (1)

Lokaci ya gabato da ba sai an tunatar da mu ba a kan abubuwan da suke faruwa da mu a duniyar nan dare da rana. Muna gani muna kuma jin abubuwan ban mamaki da suke faruwa a ko’ina a fadin duniyar nan. Kowace rana tana dauke da nata labari, wayewar kowace safiya za ka ji mutane da dama sun rasa rayukansu ko muhallinsu ko ’yan uwansu ko dukiyarsu; ana niyyar yaki a nan, an fara yaki a can, an yi girgizar kasa a wuri kaza da sauransu. Ma su bi da dama sun manta da abubuwan da Yesu Almasihu ya fada lokacin da almajiransa suka tambaye shi alamun dawowarsa da ta karshen zamani? 

“Yana zaune a kan Dutsen Zaitun sai almajiransa suka zo wurinsa a kadaice, suka ce, “Gaya mana, yaushe za a yi wadannan abubuwa? Mece ce kuma alamar dawowarka da ta karewar zamani?” Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku kula fa kada kowa ya batar da ku, domin mutane da yawa za su zo da sunana, suna cewa, su ne Almasihu, har su batar da mutane da yawa. Za ku kuma rika jin labarin yake-yake da jita-jitarsu. Kada fa hankalinku ya tashi, don lallai ne a yi haka, amma karshen tukuna. Al’umma za ta tasar wa al’umma, mulki ya tasar wa mulki. Za a kuma yi yunwa da raurawar kasa a wurare daban-daban. Amma fa duk wannan masomin azaba ne tukuna.

“Sa’an nan za su bashe ku, a kuntata muku, su kuma kashe ku. Duk al’ummai za su ki ku saboda sunana. A sa’an nan da yawa za su yi tuntube, su ci amanar juna, su kuma ki juna. “Annabawan karya da yawa za su firfito, su batar da mutane da yawa. Saboda kuma yaduwar mugun aiki, sai kaunar yawancin mutane ta yi sanyi. Amma duk wanda ya jure har karshe, zai samu ceto. Za a kuma yi bisharar nan ta Mulkin Sama ko’ina a duniya domin shaida ga dukan al’ummai. Sa’an nan kuma sai karshen ya zo.” Matiyu 24:9-14 Yesu Almasihu ya ba da wasu alamu da yake so mu lura da su. 

1. Annabawan karya

Mun sha gani mun kuma san cewa annabawan karya suna nan tare da mu, har ma da yawa sun fito suna cewa su ne Almasihu, a kasashen waje, cikin Afirka har ma nan Najeriya, mun shaida wannan, akwai kuma fastocin karya wadannda suna nan ba iyaka, suna ta yin abubuwan al’ajibi, su rinjayi mutane da dama sun raba su da koyarwar Yesu Almasihu, dalili kuwa shi ne muna cikin lokacin da mutane ke son jin abubuwan da za su gamsar da su, su biya musu muradinsu domin sun sa kwadayin kayan duniya fiye da bin Allah. “Domin lokaci zai zo da mutane ba za su jure sahihiyar koyarwa ba, amma saboda kunnensu yana kaikayi, sai su taro masu koyarwa da za su biya musu muradinsu. Za su toshe kunnensu su koma ga jin tatsuniyoyi.” 2 Timoti 4:3-4. Ta dalilin haka ne za ka ga masu bi da dama sun bar bautar Ubangiji sun koma bauta ea annabawan karya, fastoci da wasu kungiyoyi, ba sa karanta Littafi Mai tsarki balle su san me Ubangiji ke fadi a kan irin wannan lokaci. Mu karanta Littafi Mai tsarki don mu zamo da sani mu kuma iya bambanta annabawa da fastoci da kuma koyarwar karya. Littafi Mai tsarki yana cewa, “Mutanena sun lalace saboda jahilci. Tunda yake sun ki ilimi…” Yusha’u 4:6. Sai mu tambayi kanmu a zamanka na mai bin Yesu Almasihu, kana da cikakken sanin Littafi Mai tsarki ko kuwa sai abin da fasto ko wani ya fadi? Ka himmatu, ka mika kanka yardajje ga Allah, yau!

2.  Yake-yake

A zamaninmu na yau kananan yara ma sun san me ake nufi da yaki. Dare da rana, kowace wayewar gari za ka ji a labarai an kashe mutane kaza an gwabza fada a tsakanin bangaren kasa kaza da kaza ko tsakanin al’umma kaza da kaza, irin wadannan labaran ba sababi ba ne gare mu. Cikar annabci ke nan fa. Amma Yesu Almasihu ya ce mana “Kada fa hankalinku ya tashi, domin lallai ne a yi haka,” abu mafi muhimmanci shi ne mu natsu mu kuma yi addu’a ba fasawa. 

“karshen dukan abubuwa ya gabato. Saboda haka, sai ku kanku ku natsu, domin ku yi addu’a. Fiye da komai kuma, ku himmantu ga kaunar juna, domin kauna takan yafe laifuffuka masu dimbin yawa. Ku rika yi wa juna bakunta, ba tare da kunkune ba. Duk baiwar da mutum ya samu, ya yi amfani da ita ga kyautata wa dan uwansa, a kan amintacce mai rikon amanar alherin Allah iri-iri ne. Duk mai wa’azi ya dai san fadar Allah yake yi. Duk mai yin hidima, ya yi da karfin da Allah Ya ba shi, domin a cikin al’amura duka a daukaka Allah ta wurin Yesu Almasihu. daukaka da mulki sun tabbata a gare shi har abadan abadin. Amin! Amin! 1 Bitrus 4:7-11.

Za mu ci gaba mako mai zuwa da yardar Ubangiji.

 

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos