‘Kwanan nan Najeriya za ta fara fitar da motocin da ta kera zuwa ketare’
Ya ce Najeriya ma ba za a barta a baya ba, yayin da kashe kere-kere.
Shugaban Hukumar Bunkasa Fasahar Kera Motoci ta Kasa (NADDC), Injiniya Jelani Aliyu, ya ce kwanan nan Najeriya za ta fara fitar da motocin da take harhadawa zuwa sauran kasashen Afirka.
Ya bayyana hakan ne yayin wani zauren tattaunawa a wajen taron hadin kai na kasuwanci da ya gudana a birnin Durban na Afirka ta Kudu.
Taron dai an shirya shi ne da nufin hada kan kasashe 55 waje daya, domin su nuna kayayyakin da suke sarrafawa a kasashensu don tallata su a fadin Nahiyar Afirka.
A cewar Shugaban na NADDC, Najeriya kuma na nan a kan bakarta ta kera motoci masu aiki da wutar lantarki domin amfaninta da ma na sauran kasashen Afirka.
Jelani ya ce hakan zai taka muhimmiyar rawa wajen samar da karin ayyukan yi.
Ya ce ba zai yiwu a bar Najeriya a baya ba, a daidai lokacin da sauran kasashe suke rige-rigen yin bajinta iri-iri a bangaren fasaha.