Kwanan nan takin Uriya zai mamaye kasuwannin kasar nan

Nan da watanni biyu masu zuwa ne ake sa ran takin Uriya zai  cika kasuwannin kasar nar a sakamakon wani sabon katafaren kamfanin taki da kamfanin  Indorama Eleme Pterochemicals zai bude a Fatakwal  a cikin watan Afirilun da za a shiga.Yanzu haka har an kammala dukkan muhimman sassa na kanfanin takin, ta yadda za a […]

Kwanan nan takin Uriya zai mamaye kasuwannin kasar nan
Kwanan nan takin Uriya zai mamaye kasuwannin kasar nan

Nan da watanni biyu masu zuwa ne ake sa ran takin Uriya zai  cika kasuwannin kasar nar a sakamakon wani sabon katafaren kamfanin taki da kamfanin  Indorama Eleme Pterochemicals zai bude a Fatakwal  a cikin watan Afirilun da za a shiga.
Yanzu haka har an kammala dukkan muhimman sassa na kanfanin takin, ta yadda za a fara gwada aikinsu, daga bisani kuma a yi bikin kaddamar da kamfanin domin ci gaba da aiki gadan-gadan.
Baya ga muhimman sassan kamfanin da aka kammala aikinsu, haka kuma an kammala aikin  bututun iskar gas mai tsawon kilomita 84 da zai samar da wadataccen iskar gas ga kamfanin, da kuma tashar daukar  takin domin fitar da shi kasashen ketare da aka samar a tashar jirgin ruwa na Onne a Fatakwal a kan kudi dala miliyan 130.
Wannan kamfanin takin idan ya fara aiki zai rika samar da ton dubu 4 na takin Uriya a kowace rana, ko kuma  ton Miliyan 14 na takin a duk wata.
Kamfanin takin dai da farko mallakar kamfanin mai na NNPC ne, kafin gwamnati ta sayar da shi  a shekarar 2005, inda kamafanin Dangote ya taya kamfanin a kan dala miliyan 135, amma kamfanin Indorama ya buge shi, inda ya taya kamfanin a kan dala miliyan 215.
A halin yanzu dai kamfanin Indorama yana da kashi 65 na hannun jarin kamfanin, kamfanin NNPC  yana da kashi 10,gwamnatin jihar Ribas tana da kashi 10, al’ummomin yankin da  aka kafa kamfanin a wurinsu suna da kashi 7 da rabi, gwamnatin tarayya tana da kashi 5, su kuma ma’aikatan kamfanin suna da kashi 2 da rabi.
Kamar yadda shugaban kamfanin Mista Munish Mundra, wani dan kasar Indiya, ya bayyana wa manema labarai a lokacin da suka ziyarci kamfanin, ya nuna cewa, kamfanin zai bunkasa harkar noma a kasar nan, domin zai samar da wadataccen takin da manoman da ke fadin kasar nan ke bukata. Kuma zai taimaka wajen yaki da yunwa da talauci da kuma samar da dimbin ayyukan yi.
Haka kuma Mista Mundra ya yi imanin cewa kamfanin takin zai daukaka matsayin Najeriya a idon duniya, saboda kamfanin takin shi ne zai  kasance a kan gaba wajen samar da takin Uriya a duniya.
Shugaban kamfanin takin ya ce an kashe zunzurutun kudi dalar Amurka biliyan daya da miliyan 400 (1.4b) wajen kafa kamfanin, inda wata cibiyar kudi ta bankin duniya mai suna International Finance Corporation (IFC) ta bayar da mafi yawan kudin, a yayin da wadansu bankunan Najeriya kuma suka taimaka da wani bangare na kudin.
Idan kamfanin ya samar da takin na Uriya, tireloli ne za su rika daukar takin da aka tara a cikin wani makeken rumbu, inda cikin minti hudu za a yi wa tirela lodi ta fita domin kaiwa sassan kasar nan, a yayin da wadansu tirelolin kuma za su dauki takin su kai tashar jirgin ruwa ta Onne domin zubawa a jirgin ruwa a kai kasashen waje. Kamar  yadda aka nuna, za a rika fitar da ton miliyan daya da dubu dari shida ne na takin Uriya.
A cewar shugaban kamfanin Mista Mundra,  za su tabbatar farashin takin Uriya ya ragu sosai daga Naira  dubu biyar zuwa sama da ake sayarwa a hakin yanzu, domin za su rika hulda ne kai tsaye da manoma tare da ilmantar da su alfanun da ke tattare da noman amfanin gonan da ke samar da kudi.
Ya ci gaba da cewa, baya ga takin Uriya, nan gaba kadan kuma za su fara samar da takin NPK,  wanda hakan zai  sanya Najeriya ta zama a sahun gaba wajen samar da takin Uriya da NPK a duniya.
Sai  dai kuma ya bukaci manoma su cire tsoron da suke da shi game da takin zamani, musammnan takin NPK, wanda ake ganin kamar yana da illa ga kasar noma. Ya ce da takin Uriya da takin NPK  duk babu mai illa a cikinsu, yadda ake samar da shi ne yake jawo illa, saboda  ba a bin ka’ida ba, watau ana rage sinadaren hada shi. Ya ce yadda takin Uriya yake  taimaka wa kasar noma saboda daga tsirrai da sauran abubuwan da dabbobi ke samarwa ne ake samunsa, haka takin  NPK  yake  da amfani. ’’Duk takin da za mu samar  zai zama mai inganci ne wanda zai taimaka wa kasar noma,  ba ya la’antata ba.’’
Wannan kamfani na takin zamani da kamfanin Indorama ya bude a Eleme ta jihar Ribas katafaren kamfani ne na zamani, gari guda ne da ke da manyan kofofin shigarsa  guda biyar, kowanne  da jami’an tsaro da kuma na’urorin tsaro, sannan akwai babban ofishin ‘yan sanda da banki da  babban ofishin  kashe gobara da kuma bangaren samar da wutar lantarki nasu na kansu da ake samarwa ta hanyar iskar gas da suke amfani da shi wajen samar da takin zamanin..  Saboda  girman kamfanin zai yi wahala a iya zagaya shi a kasa, sai dai  a kan abun hawa.
Indorama dai kamfani ne mallakar mutanen kasar Indonesiya, kalmomi biyu ne aka hada a wuri daya, watau Indo, wanda ke nufin Indonesiya da kuma Rama, wanda suna wani sarki ne a kasar Thailand.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya