Kwanan nan wasu gwamnonin APC za su dawo PDP- Shugaban PDP
Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Chief Uche Secondus y ace wasu gwamnonin da aka zaba a karkashin inuwar Jam’iyyar APC a yankin Arewa ta Tsakiya suna shirin dawowa Jam’iyyar PDP. Secondus ya ce tuni suka riga suka fara shirye-shirye da tattaunawa da gwamnonin. Gwamnan ya yi wannan jawabin ne a Umuahia na Jihar Abiya a […]
Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Chief Uche Secondus y ace wasu gwamnonin da aka zaba a karkashin inuwar Jam’iyyar APC a yankin Arewa ta Tsakiya suna shirin dawowa Jam’iyyar PDP.
Secondus ya ce tuni suka riga suka fara shirye-shirye da tattaunawa da gwamnonin.
Gwamnan ya yi wannan jawabin ne a Umuahia na Jihar Abiya a lokacin day a kai ziyarar kwanan daya a jihar.
Gwamnan ya kara da cewa yanzu haka akwai rikici a cikin jam’iyyar ta APC, sannan kuma kasa babu man fetur kuma babu abinci, “Mun zo aikin ceto ne,” inji shi.