Kwanan nan za a dawo da aikin Umarah —Saudiyya
Karon farko da za a dawo da ibadar bayan dakatar da ita na tsawon watanni saboda COVID-19
Ministan Aikin Hajji da Umarah na kasar Saudiyya, Dakta Mohammad Saleh bin Taher Benten ya ce nan ba da jimawa ba za a dawo da ibadar Umarah kamar yadda aka saba yi a baya.
Wannan shi ne karon farko da za a dawo da ibadar bayan dakatar da ita tsawon watanni saboda barazanar cutar COVID-19.
- Saudiyya na duba yiwuwar dakatar da aikin Hajjin bana
- Mazauna Saudiyya be kadai za su yi aikin Hajjin bana
Ministan ya tabbatar da hakan ne a ranar Talata, lokacin da yake jawabi a wani taron masu ruwa da tsaki kan bunkasa harkokin aikin Hajji karo na biyu da ya gudana ta fasahar bidiyo.
Ya ce, “A kokarin da muke yi na sassauta dokkokinmu tare da komawa ibadun Umarah da ziyara kamar yadda aka saba, ma’aikatarmu za ta bullo da matakan da za su ba kamfanoni da hukumomi damar dawo da harkokin ibadar yadda ya kamata.
“Nan ba da jimawa ba masarautar Saudiyya za ta dawo da ayyukan Umarah da zai rika gudana cikin matakan kiyaye lafiya da kuma kariya”, inji shi.
Ministan ya kuma tabbatar da cewa kasar za ta kirkiro wata manhaja da za ta bai wa duk wani mai son yin Umarah amfani da ita domin zabar lokacin da zai gudanar da ibadar.
Hakan dai na nufin takaita yawan mutanen da za su gudanar da ibadar lokaci guda a domin tabbatar da bayar da tazara da rashin cunkoso.
Idan dai za a iya tunawa, a bana hatta aikin Hajji mutane 10,000 ne kacal aka bari suka yi sabanin sama da miliyan biyu a bara.