Kwanan nan za a fara kashe kudaden Najeriya a China
Bankunan Najeriya da China za su fara aiki a kasashen biyu.
Bankunan kasar China za su fara karbar kudaden Najeriya nan gaba, kuma bankunan China za su shigo Najeriya domin fara aiki.
Jakandan kasar China a Najeriya, Cui Jianchun, ya sanar da cewa hakan zai taimaka wajen bunkasawa tare da saukaka gudanar da harkokin kasuwanci da zuba jari a tsakanin kasashen biyu.
- Gwamnati ta yi gwanjon rigar nonon Diezani a kan $12.3
- Boko Haram ta mayar da masana’antar bom dinta Kaduna
Ya ce ofishinsa na aiki ka’in da na’in domin tabbatar da ganin bankunan Najeriya sun fara aiki a kasashen biyu, kuma “Manyan bankunan kasashen biyu na kokarin fara aiwatar da yarjejeniyar amfani da kudadensu a tsakaninsu; kuma za a fadada tsarin.
“Yanzu haka ina aiki domin ganin bankunan kasar sun shigo Najeriya sun fara aiki, bankunan Najeriya ma suna aiki a China,” inji shi.
Da yake bayani a wata tattaunawa da manema labaria a Abuja, hakan zai saukaka amfani da kudaden China da Najeriya a tsakaninsu wajen gudanar da kasuwanci da harkar masana’antu.
Mista Jianchun, ya yi fatan samun fahimtar juna tsakananin majalisun dokokin kasashen biyu a kan hakan.
Ya ce a watan Nuwamba mai kamawa ne za a gudanar ta taron ministocin kungiyar hadin kan kasashen Afirka da China karo na takwas a kasar Senegal.