Kwanan nan za mu tantance malaman sakandiren Kaduna- Gwamna El-Rufa’i
Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya bayyana cewa kwanannan za su gudanar da jarabawar kwarewa ga malaman makarantun sakandiren jihar. Gwamnan ya bayyana haka ne a kafar sandarwarsa ta tiwita a ranar Lahadi. Ya ce jihar ta mayar da hankali wajen dawo da martabar ilimi a bangaren koyarwa. Ya bayyana cewa gwamnatin […]

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya bayyana cewa kwanannan za su gudanar da jarabawar kwarewa ga malaman makarantun sakandiren jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne a kafar sandarwarsa ta tiwita a ranar Lahadi.
Ya ce jihar ta mayar da hankali wajen dawo da martabar ilimi a bangaren koyarwa.
Ya bayyana cewa gwamnatin ta amince ta biya malaman da ke koyarwa a birnin jihar kashi 27 da rabi fiye da albashin matsakaicin ma’aikacin gwamnati sannan kuma za ta biya malaman da ke koyarwa a kauyuka kashi 32 da rabi don kwadaitar da kwararru masu sha’awa.